Rashin shugabanci nagari shi ne matsalar Nijeriya – Hon Sarki Aliyu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon Sarki Aliyu Daneji, ɗan majalisar jiha mai wakiltar birnin Kano da kewaye ya bayyana cewa babbar matsalar Nijeriya rashin samun ingantaccen shugabanci da ƙasar ke samun kan ta a haka.

Daneji ya ce hakan ya sa za ka ga kullum an yabi su Sardaunan Sokoto da Tafawa Balewa da su Malam Aminu Kano da dai shugabanni wanda suka taka rawar gani wajen cigaban ƙasa da al’ummarta ta hanyar riƙon amana da rashin fifita buƙatunsu akan na talakawa, wanda ya ce hakan ya sa ba sa alfahari da abin da suka tara sun fi son a tuna su da nagarta da kyakkyawan yabo da addu’a ko bayan ransu shi ne shugabanci nagari.

Haka kuma ya ce yanzu dai su a Kano suna farin ciki da samun magajin Malam Aminu Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ko masu hamayya da shi sun yadda cewa mutum ne mai kishin bunƙasa ilimi wanda shi ne gwamna wanda ya samar da jami’o’i biyu ga kuma yin magana ɗaya a dukkan wani lamarin shi an san shi da kishin ga matasa da sauran al’ummar Kano da Nijeriya baki ɗaya, sai kuma shi kansa gwamna Abba kowa ya tabbatar cewa tsarinsa irin na madugun siyasar Kano da Arewa ne don haka muna ganin shugabanci nagari da ake buƙatar matasa soyi koyi da yan mazan jiya da yau managarta.

A ƙarshen ya yaba wa gwamnati Abba a kan wannan tunanin na horar matasa yadda ake yin shugabanci na gari ya kuma yi nasiha kan matasa zama mutane nagari ta hanyar kyakyawar mu’amama da girmama na gaba da tausayin juna da kuma kawar da yaudara da ƙarya da wasu matasan ke ganin ba komai ba ne kuma babbar ila ce a kama matasa a wannan ɗabi’a ta ƙarya da yaudara da sauran miyagun ɗabi’u kasancewar su shugabannin gobe wajibi ne.

Taron dai ya samu halartar shugabanni da masana da suka gabatar da takardu domin samar da matasa nagari, cikin su har da Matamakin Shugaban Jami’ar Khairun Farfesa Abdulrashid Garba da sauransu.

By ukarofi