
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa (NERC) ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su biya Naira biliyan 20.33 da ake bin su na kuɗaɗen mita ga kwastomomi cikin shekara guda.
Za a dawo da kuɗaɗen ne, waɗanda ta ce lissafi su zai fara ne tun daga ranar 1 ga watan Maris, 2026.
Wannan kuɗi ya shafi tsarin samar da mita na masu zaman kansu (Meter Asset Provider MAP), inda kwastomomi suka biya kuɗin sayen mita da kansu, domin a mayar musu da kuɗin daga baya.
Hukumar ta bayar da wannan umarni ne a cikin wata takarda mai kwanan wata 1 ga Maris, mai taken: “Gyaran umarni kan mayar da kuɗin mita ga kwastomomi.”
Hukumar ta yanke wannan mataki ne duba da cewa ta lura tsarin dawo da kuɗaɗen na fama da jinkiri daga kamfanonin, don haka ta bayar da sabon umarni.
