
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Laraba Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin sufeto janar na rundunar ‘yan sandan Nijeriya (IGP) na 23.
An gudanar da taron rantsarwar ne a sashen majalisa na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne gabanin zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), sannan ya samu halartar ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.
An fara zaman na FEC ne jim-kaɗan da kamar taron rantsarwar.
Waɗanda suka samu halarta sun haɗa da Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu; da kuma Misis Esther Walson-Jack, wato Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata.
