
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ɗage sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Abubakar Malami da ɗansa Abdulaziz ta zargin su da tallafa wa ta’addanci zuwa ranar 10 ga watan Maris, 2026.
Matakin ya biyo bayan buƙatar shugaban masu gabatar da ƙararraki na Nijeriya, Rotimi Oyedepo, wanda ya ce an sauya shari’ar daga hannun DSS zuwa ofishinsa, don haka yana bukatar karin lokaci domin nazarin takardun karar.
Lauyan wadanda ake kara bai yi adawa da dagewar ba, amma ya bukaci kotu ta soke karar idan masu kara ba su fara gabatar da shaidu a ranar da aka sanya ba.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da ɗagewar tare da umartar masu ƙara su fara shari’a a ranar da aka ayyana.
