Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ga Musulmin duniya, watan Ramadan wata ne mai tsarki kuma mai cike da alfarma, wanda ya ƙunshi manyan abubuwa masu muhimmanci a tarihin Musulunci. Wata ne na ibada, tausayi da kusantar Allah, inda Musulmai ke gudanar da azumi – ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci guda biyar.
Baya ga kasancewarsa watan ibada da tsarkake zuciya, Ramadan ita ce wata ta tara a kalandar Musulunci, kuma ta zamo shaida ga muhimman abubuwa da suka sauya akalar tarihin addinin Islama.
Saukar da Al-ƙur’ani:
Mafi girman abin da ya faru a watan Ramadan shi ne saukar da Al-ƙur’ani mai tsarki ga Annabi Muhammad (SAWW). Allah Maɗaukaki Ya bayyana cewa an saukar da Al-ƙur’ani a cikin wannan wata, kuma farkon wahayi ya sauka ne a daren Lailatul-ƙadr – daren da darajarsa ta fi ta wata dubu.
Wannan lamari ya sanya Ramadan ta zama wata na haske da shiriya ga bil’adama baki ɗaya.
Yaƙin Badar:
A ranar 17 ga watan Ramadan, shekara ta biyu bayan Hijira, aka gwabza Yaƙin Badar – yaƙi na farko tsakanin Musulmai da mushrikai. Duk da ƙarancin rundunar Musulmai, Allah Ya ba su nasara a kan maƙiyansu da suka fi su yawa da kayan aiki.
Sahabbai 14 ne suka yi shahada a wannan yaƙi. A yaƙin an kashe Abu Jahl, ɗaya daga cikin manyan maƙiyan Manzon Allah. Wannan nasara ta ƙarfafa Musulunci tare da tabbatar da ƙarfin imani da tawakkali.
Fathul Makkah (ƙwace Makkah):
A ranar 18 ga Ramadan, shekara ta takwas bayan Hijira, Annabi (SAWW) ya shiga Makkah tare da runduna domin karɓe ikon birnin. An samu nasara cikin lumana ba tare da zubar da jini ba.
Wannan lamari ya kawo ƙarshen bautar gumaka a Makkah, tare da buɗe babi na sabuwar daular Musulunci. Mutane da dama sun rungumi addinin Musulunci bayan wannan nasara mai tarihi.
Rasuwar Nana Khadija (AS):
A ranar 10 ga Ramadan ne Nana Khadija (AS), matar Manzon Allah ta farko, ta rasu. Ita ce ta farko da ta amince da saƙon Musulunci, kuma ta kasance ginshiƙi mai ƙarfi wajen tallafawa Manzon Allah a farkon wahayi.
Rasuwarta ta kasance babbar rashi ga al’ummar Musulmi.
Rasuwar Nana A’isha (RA):
A shekara ta 58 bayan Hijira, a ranar 17 ga Ramadan, Nana A’isha (RA), matar manzon Allah, ta rasu. Ta kasance ɗaya daga cikin manyan masu ruwaito Hadisai, inda malamai da dama suka bayyana cewa kaso mai yawa na ilimin fikihu da Hadisi ya iso ne ta hannunta.
Shahadar Sayyidina Ali (AS):
A ranar 19 ga Ramadan, shekara ta 40 bayan Hijira, aka kai wa Imam Ali bin Abi Talib (AS) hari a masallacin Kufa yayin da yake jagorantar sallar asuba. Abdurrahman bn Muljam ne ya sare shi da takobi mai guba a goshi.
Imam Ali (AS) ya yi shahada a ranar 21 ga Ramadan sakamakon raunin da ya samu. An ruwaito cewa kalamarsa ta farko bayan an sare shi ita ce: “Fuztu wa Rabbil Ka’aba” – na yi rabo da Ubangijin Ka’aba.
Kafin rasuwarsa, ya yi wasiyya da a yi adalci ga makashinsa, kada a azabtar da shi fiye da hukuncin da ya dace. Wannan ya nuna girman adalcinsa da karamcinsa, har ma ga maƙiyansa.
Shahadarsa ta kasance babban rashi ga Musulunci, domin ya kasance gwarzon jihadi, ilimi da adalci bayan Manzon Allah (SAW).
Yaƙin Tabuk:
Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a watan Ramadan akwai shirin Yaƙin Tabuk, wanda ya nuna ƙarfin Musulunci a fuskantar barazanar waje. Haka kuma, Annabi (SAWW) ya tura Imam Ali (AS) zuwa Yemen domin jagorantar runduna, inda mutane da dama suka karɓi Musulunci.
Ramadan wata ne da ya ƙunshi tarihi mai zurfi da darussa masu yawa ga al’ummar Musulmi. Wata ne da ya haɗa ibada da gwagwarmaya, nasara da jarrabawa, haƙuri da tawakkali.
Yin nazari kan waɗannan abubuwa yana ƙara mana fahimtar muhimmancin watan Ramadan, tare da zaburar da mu mu cika shi da ibada, kyautata ɗabi’a da kuma koyi da darussan da tarihin Musulunci ya gada mana.
