Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Next Frontiers Hub Initiative (NFHI) ta halarci wani babban taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja ranar 4 ga Agustan 2026, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi bunƙasa hada-hadar kuɗi, rage talauci, ƙarfafa matasa da kuma ci gaba mai ɗorewa a Nijeriya.
Wacce ta kafa ƙungiyar kuma shugabarta, Dakta Fatima Usman Nazir, ce ta wakilci NFHI a taron.
A yayin taron, ta yi mu’amala da sarakunan gargajiya, shugabannin cibiyoyin kuɗi, masu tsara manufofi da sauran fitattun masu ruwa da tsaki.
Taron ya samar da wata muhimmiyar dama ta tattaunawa, haɗin gwiwa da ƙulla alaƙa kan dabarun da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
A yayin zaman tattaunawar, Dakta Fatima Usman Nazir ta gana da manyan masu ruwa da tsaki a fannonin kuɗaɗen Musulunci (Islamic Finance), Inshorar Takaful da kuma cibiyoyin gargajiya, inda suka tattauna hanyoyin haɗin gwiwa domin ƙarfafa matasa da rage talauci.
Har ila yau, an gudanar da zaman fasaha kan batutuwa da suka haɗa da rawar da Inshorar Takaful za ta taka wajen rage talauci, inganta jin daɗin ma’aikatan gwamnati da kuma tallafa wa cimma Manufar Nijeriya ta 2030 (Nigeria Vision 2030).
ƙungiyar ta bayyana cewa waɗannan batutuwa sun yi daidai da manufofinta na bunƙasa dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki, tabbatar da haɗin kan al’umma da kuma inganta walwalar jama’a.
Halarcin taron ya kuma bai wa NFHI damar ƙara bayyana ayyukanta a gaban manyan masu ruwa da tsaki, lamarin da ake sa ran zai buɗe ƙofofin sabbin haɗin gwiwa a fannoni irin su kuɗaɗen da suka ginu kan ɗabi’a, walwalar al’umma da bunƙasa matasa.
ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka ɗauki hankali a taron shi ne rabon cak ga masu amfani da inshora daga Kamfanin Crown Takaful, a matsayin wani mataki na nuna jajircewarsa wajen kula da muradun kwastomomi da kuma tallafa wa ci gaban al’umma.
NFHI ta bayyana cewa sakamakon tattaunawar da aka yi a taron ya ƙara ƙarfafa ƙudurinta na mai da hankali kan:
ƙarfafa tattalin arzikin matasa.
Tallafa wa ilimi da lafiyar yara mata.
Samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.
Da yake jawabi bayan kammala taron, ƙungiyar ta sake jaddada aniyarta ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Kamfanin Crown Takaful da sauran masu ruwa da tsaki domin aiwatar da shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar matasa, kasuwanci, hada-hadar kuɗi da walwalar al’umma.
ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da aiki bisa manufarta ta “ƙarfafa Matasa, Gina Zaman Lafiya da Farfaɗo da Rayuwa,” tare da gina haɗin gwiwar dabaru da za su taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a sassa daban-daban na Nijeriya.
