Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da Majalisar Tarayya a rubuce shawarar ƙungiyar ECOWAS ta bayar na ɗaukar matakin soji s’a kan Jamhuriyar Nijar.
Wasiƙar Tinubu ga Majalisar ta ƙunshi har da neman izinin tura sojojin Nijeriya zuwa Nijar kamar yadda ECOWAS ta yanke.
Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ya aike wa Majalisar wadda Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanto a zauren majalisar.
Sanarwar ta nuna ECOWAS ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubun ta yi tir da matakin juyin mulkin da sojoji suka ɗauka a ƙasar ta Nijar.
Ta ƙara da cewa, biyo bayan taron da ECOWAS ta yi, ƙungiyar ta amince da a ɗauki matakin da zai ba da damar maida zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijar, Bazoum kan mulkin ƙasar.
Daga cikin shawarwarin da taron na ECOWAS ya bayar, har da “Rufewa da sanya idon kan dukkanin iyakokin ƙasa da Nijar….”
“Katse bai wa ƙasar wutar lantarki. Neman goyon bayan sauran ƙasashen duniya wajen aiwatar da sakamakon taron ECOWAS, hana shiga da fitar jiragen sama a ƙasar.
“Tura dakaru don tilasta wa sojojin yin abin da ya kamata muddin suka ƙi ba da kai bori ya hau” da sauransu in ji sanarwar.