Nijeriya ta ware fiye da naira biliyan huɗu don yaƙi da HIV

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta amince da kashe naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a ƙasar.

Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta tarayya, inda gwamnatin ta sanar da ware fiye da dala biliyan ɗaya ga vangaren lafiyar ƙasar.

Gwamnatin ta ce wannan yana daga cikin manufofinta na inganta kiwon lafiya a matakin farko.

Ta ce ta tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da bayar da horo gare su domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta kamata don hana yaɗuwar cutar HIV a sassan ƙasar.

A baya dai an riƙa bayyana damuwa game da sabbin tsare-tsaren da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta vullo da su, musamman a fannin bayar da tallafi, inda ake tunanin za su iya shafar tallafi ga yaƙi da cutar HIV a ƙasashe masu tasowa.

Amma a ranar Asabar gwamnatin Amurkan ta sanar da ware sabon ƙunshin tallafin yaƙi da cutar ta HIV.

Alƙalumman da hukumar hana yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya ta fitar, sun ce ƙasar ce ta fi kowacce yawan masu cutar a yammacin Afirka, kuma an daɗe ana samun kiraye-kiraye daga faɗin duniya na ganin Nijeriya ta zage damtse wajen yaƙi da yaɗuwar cutar.

By ukarofi