Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudurinta na kawo sauye-sauye a ɓangarori da dama domin sauƙaƙawa ’yan ƙasa.
Gwamnatin Tinubu ta ce, za ta cire laifin yunƙurin kashe kai a Nijeriya, tare da sanya watan Disamba 2025 a matsayin wa’adin aiwatar da gyaran.
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, yayin bikin ranar hana kashe kai ta duniya.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, sama da mutum 720,000 ke mutuwa sanadiyyar kashe kai kowace shekara, mafi yawansu daga ƙasashe masu tasowa.
A Nijeriya, babban shinge ga neman taimako shi ne sanya yunƙurin kashe kai cikin kundin laifi, abin da ya ƙara tsangwama da tozarta masu rauni daga cikinsu.
Don magance wannan matsalar, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin kasa a ranar 10 ga Oktoba 2024, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Cheluchi Onyemelukwe.
Pate, wanda babbar sakatariyar ma’aikatar, Daju Kachollom ta wakilta, ya ce, “An tabbatar da cewa idan an ƙara wayar da kai da kulawa, kisan kai zai ragu sosai, Taken bana shi ne kira da mu maye gurbin rashin magana da tattaunawa, kunya da tausayi, sannan mu gane kalmominmu suna da tasiri.”
Ali Pate ya ce, gwamnati ta riga ta fitar da takardar manufofi, tare da kammala ƙudirin dokar gyara kan dokar lafiyar kwakwalwa ta 2021.
“Bayan haka, zan gabatar da takarda a fadar majalisar zartarwa don samar da ƙudirin dokar cire laifin yunƙurin kashe kai,” inji Farfesa Ali Pate.
A nata jawabin, Kachollom ta ce, “Haƙiƙanin gaskiya shi ne, sanya yunƙurin kashe kai cikin laifi ba ya ceton rai, sai ƙara tsananta matsalar.”
Shugaban shirin lafiyar kwakwalwa ta ƙasa, Dr. Tunde Ojo, ya ce gyaran ya dace da tsarin duniya inda ake ɗaukar kashe kai a matsayin matsalar lafiya.
A saƙonta kan lamarin, Daraktar CHAI a Nijeriya, Dr. Olufunke Fasawe, ta ce Nijeriya ta na matsayi na bakwai a duniya kan yawan kashe kai.
