Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanonin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, da Kamfanin Chevron sun yi wani gagarumin aikin gano sabon wurin ɗanyen mai kusa da rijiyar haƙar mai ta Meji NW-1 a yankin Neja Delta ta yamma.
Yankin, wanda a ka canja kwanan nan zuwa PIA 2021, wani muhimmin yanki ne mai albarkatun mai a Nijeriya.
Hakan zai kara inganta harkokin makamashi a Nijeriya da farfaɗo da tattalin arziki.
Babban manajan kamfanin Chevron, Olusoga Oduselu shi ya tabbatar da haka a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoban 2024.
Oduselu ya ce sun samu nasarar da haɗin gwiwar kamfanin NNPCL kan aikin haƙar rijiyar man.
Ya ce aƙalla sun yi nasarar tonon kafa 8,983 a cikin ƙasa a tsakiyar watan Satumbar 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rijiyar da aka haƙa za ta iya samar da aƙalla hanga 17,000 na ɗanyen mai.