NNPCL ya biya bashin Dala 2.4bn da albishirin samar da tashoshin CNG 12 a 2025

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya ce sun yi nasarar kammala biyan bashin da ake bin kamfanin daga kamfanonin mai na ƙasashen ƙetare inda ya ce a yanzu babu mai bin kamfanin bashin sisin kwabo.

Ya ce, hakan babbar nasara ce da aka cimma tun bayan cire tallafin mai a Gwamnatin Shugaba Tinubu.

“Mun riƙa karkatar da kuɗaɗenmu da dukiyoyinmu don tabbatar da komai na tafiya daidai a ɓangaren mai na PMS mai wuyar sha’ani, abinda ya rika janye hankalin NNPC daga biyan basussuka.”

Mele ya cigaba da cewa, “Sai dai yanzu wannan matsala ta kau. Za ku ga cewa ba mu da wani bashin da ake bin mu, kuma don mu tabbatar da ɗorewar hakan, ya zama wajibi a kawar da duk wata matsala don masana’antar ta iya samar da makamashi mai ɗorewa da arha da ake buƙata a ƙasar nan.”

Shugaban NNPC ɗin ya kuma tabbatar da cewa, zuwa ƙarshen rubu’in farko na shekarar 2025, za a samu aƙalla manyan tashoshin rarraba gas ta CNG har guda 12 a faɗin ƙasar.

“A cikin rubu’in farko na 2025, za a samar da akalla tashoshi 12 na CNG, har ma da gina ƙaramar masana’antar LNG da za ta riƙa samar da iskar gas ɗin al’amuran yau da kullun a kasuwa, da kuma sauƙaƙa rarraba CNG mai inganci da iskar gas ga ƙananan turakun samar da wutar lantarki a cikin wannan masana’anta a ɗan ƙanƙanin lokaci.”