Daga AMINA YUSUF ALI
Kamfanin rarraba man fetur a Nijeriya (NNPCL) ya yi wa wasu daga cikin manyan ma’aikatansa/ shugabannin kamfanin ritayar dole. Wato ya tilasta wa wasu manyan ma’akatansa da wa’adin yin ritayar aikinsu ba ta wuce nan da watanni 15 masu zuwa ba yin ritayar dole.
Wannan jawabin yana ƙunshe ne a cikin wani jawabi da hukumar gudanarwar ta kamfanin ta bayar a ranar Litinin ɗin da ta gabata ranar 18 ga Satumba, 2023, sannan ta wallafa a asusunta na shafin X (wanda da aka fi sani da Tiwita) a safiyar ranar Talata.
Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa, sallamar tasu ko ritayar dolen da aka yi musu za ta fara aiki ne daga ranar Talata, 19 ga watan Satumban 2023.
Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan hukuncin ya zama dole saboda akwai wasu manunfofi na bunƙasa kasuwanci da kamfanin na NNPCL yake son cimmawa. Kuma kafin cimma nasarar a cewar jawabin, dole sai an samar da masu jini a jika a matsayin shugabannin gudanarwa.
In za a iya tunawa dai, a kwanakin baya kaɗan da suka wuce ne dai da ma kamfamin ya yi sabbain naɗe-naɗe da suka haɗa har da sabon mataimakin shugaban zartarwa na kamfanin wato, Oritsemeyiwa A. Eyesan.
Da kuma sauran naɗe-naɗe a qoqarinsa na ganin an bunqasa harkokin kamfanin. Tare da yin biyayya ta sau da ƙafa ga dokar masana’antar man fetur ta Nijeriya (PIA), wato ta samar da riba da kuma haraji ga asusun gwamnatin Tarayya.
Bayan waɗannan sabbin naɗe-naɗe na shugabannin zartarwar, kwamitin yana ganin akwai buƙatar a yi gaggawar saita NNPCL don samar da tsare-tsare masu amfani da kuma dabarun sayar da wasu kadarorinta.