NSCIA ta yi zargin maƙarƙashiyar addini kan tsare El-Rufai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar ƙoli ta Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai zargin cewa wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan na iya nuna akwai wasu manufofin ɓoye na addini da ke tasiri kan shari’ar.

Majalisar ta ce a baya ta guji tsoma baki cikin lamarin, saboda ta ɗauka cewa shari’ar El-Rufai wani lamari ne na shari’a da kotuna za su gudanar cikin adalci.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da Sakataren-Janar na majalisar, Farfesa Is-haƙ Oloyede, ya fitar ranar Talata, NSCIA ta ce sabbin abubuwan da suka bayyana a bainar jama’a sun sa ta sauya matsayinta.

A cewar majalisar, akwai alamun cewa wasu muradu ko manufofin ɓoye na addini na iya yin tasiri kan yadda ake gudanar da shari’ar tsohon gwamnan.

NSCIA ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ɓangaren shari’a da su hana duk wani mai irin waɗannan manufofi amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari’a wajen aiwatar da abin da ta kira manufar ɓangaranci ko ta addini a kan El-Rufai.

Haka kuma, majalisar ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji kalaman da ka iya kawo cikas ga gudanar da shari’ar cikin adalci ko kuma ƙara taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

NSCIA ta jaddada cewa ba ta neman a dakatar da shari’ar El-Rufai, sai dai tana buƙatar a tabbatar da cewa ana gudanar da ita cikin gaskiya da adalci, ba tare da tsoma bakin muradun addini ko na siyasa ba.

Wannan matsayar majalisar ta zo ne yayin da tsohon gwamnan ke fuskantar shari’o’i kan zarge-zargen da suka shafi laifukan kuɗi da kuma wasu batutuwan da suka taso dangane da lokacin da yake jagorantar Jihar Kaduna.

A ranar 31 ga Agusta, Majalisar Shari’a ta Nijeriya ita ma ta nuna damuwa kan ci gaba da tsare El-Rufai, tana mai cewa dole ne a kiyaye haƙƙinsa na tsarin mulki da kuma ƙa’idojin shari’a.

Majalisar ta kuma jaddada ƙa’idar cewa mutum ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

Lamarin ya ƙara ɗaukar hankali bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta raba kan al’ummar Kaduna, tare da zargin cewa an samu kashe-kashe a kudancin jihar a lokacin mulkinsa.

Musa ya yi wannan magana ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a farkon watan Satumba.

Sai dai, iyalan El-Rufai sun yi watsi da zarge-zargen, inda suka bai wa ministan wa’adin kwanaki bakwai da ya gabatar da hujjoji kan kalamansa ko ya janye su tare da neman afuwa.

NSCIA ta ce wajibi ne a tabbatar da cewa shari’ar tsohon gwamnan ba ta zama hanyar zurfafa rarrabuwar kawuna ta addini ko siyasa a Nijeriya ba, tana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ’yan ƙasa.

By ukarofi