NURTW: Ƙungiyar Arewa Renaissance ta nemi Alƙalin Alƙalai ta hukunta MC Oluomo bisa ƙin biyayya ga hukuncin kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ‘Arewa Renaissance Group’ ta hannun shugaban ofishinta na bincike, Haliru Nadabo, ta bayyana zaɓen Musiliu Oluomo a kujerar sabon shugaban ƙungiyar ƴan yuniyon (NURTW), a matsayin karan tsaye ga shari’a.

MC Oluomo, wanda yaron Shugaba Tinubu ne a siyaysance, an zaɓe shi ne duk da cewa Kotun Ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin ‘Industrial Court of Nigeria’ na cewa Frins Ibikunle shi ne halastaccen shugaban ƙungiyar.

Saidai, ɓangaren masu biyayya ga MC Oluomo sun je sun yi haramtaccen zaɓe a Abuja a inda suka zaɓe shi a matsayin shugaba.

Don haka ne ƙungiyar ke kira ga Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta binciki lamarin tare da ɗaukar matakan da suka dace game da rashin adalcin don kare martabar tsarin shari’a a Nijeriya.

Nadabo ya bayyana hakan ne wa manema labarai a Abuja inda ya ce ba zai bari harkar shari’a ta zama shirme ba da har za a ke mata karan tsaye.

Ya ce, lallai ne Alƙalin Alƙalai ta ɗauki mataki saboda ko shugaban ƙasa ba shi da hurumin sauya hukuncin kotu balle yaronsa na siyasa.

Nadabo ya ƙara da cewa, sanannen abu ne cewa Alhaji Frins Tajudeen Ibikunle Baruwa shi ne wanda aka sake zaɓa a matsayin shugaban NURTW.

Haka ma Antoni Janar na Ƙasa lallai sai ya tsoma baki a lamarin tare da gayyato baki ɗaya waɗanda hakan ya shafa don warware shi a shari’ance.

By Babaji