NURTW ta haɗa kai da AIRLIN don ƙarfafa matakan kiyaye afkuwar haɗurra

Spread the love

Daga MAHDI  M. MUHAMMAD

A ƙoƙarinta na cimma manyan manufofin don kyautata rayuwar ’yan Nijeriya, Ƙungiyar ‘Advocacy for Integrity and Rule of Law Initiative’ (AIRLIN) ta bayyana manufarta ta haɗa gwiwa da Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW).

Yayin da ‘yan ƙungiyar AIRLIN suka ziyarci Sakatariyar NURTW ta Jihar Nasarawa da ke Lafiya, Kodinetan ƙungiyar a Jihar, Alhaji Ibrahim L Ibrahim ya bayyana cewa AIRLIN ƙungiya ce mai zaman kanta da ba ta siyasa ko addini ba, wadda kuma ke goyon bayan ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi na inganta rayuwar al’umma ɗari bisa ɗari.

Alhaji Ibrahim ya yi tsokaci kan yaƙi da munanan ɗabi’u da sauran matsalolin zamantakewa da su ke durƙusar da Nijeriya a matsayin wasu batutuwan da ƙungiyar ke ƙoƙarin kawar da su.

Ya ce, ta haka ne ake kallon ƙungiyar ta NURTW a matsayin wata babbar cibiya da ke taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan mambobinta wajen kawar da tuƙin ganganci.

A cewar kodinetan, a wani ɓangare na aikin AIRLIN don tabbatar da kwaciyar hankalin al’umma ta sa ta haɗa kai da NURTW a wani yunƙuri na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji.

Da yake bayyana ƙarfin AIRLIN a matsayin ƙungiyar da ke da mambobi a faɗin ƙananan hukumomin Jihar Nasarawa, Ibrahim Ibrahim ya kuma buƙaci haɗin kai da rassan ƙungiyar ta NURTW a jihar, kamar yadda ya yi amfani da wannan dama wajen taya shugaban NURTW na jihar murnar samun nasararsa a zaɓukan baya-bayan nan da ƙungiyar ta gudanar.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar ta NURTW a jihar, Alhaji Abubakar Mohammed Maikwarya ya yaba wa ƙungiyar AIRLIN bisa goyon bayan gwamnati da kuma ayyana ƙungiyar ta NURTW a matsayin mai ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirin dogaro da kai.

Maikwarya wanda ya ce ƙungiyar ta NURTW ta himmatu wajen faɗakar da mambobinta game da tuƙin ganganci da kuma yin lodin kaya na wuce kima, ya ce tare da haɗin gwiwar AIRLIN za a ƙara samun nasara.

Shugaban NURTW na Jihar ya bada tabbacin cewa ƙungiyarsa za ta haɗa kai da AIRLIN a yayin gangamin wayar da kan jama’a da ke tafe cikin ƙanƙanin lokaci, yana mai tabbatar wa AIRLIN cewa ƙofarsa a buɗe ta ke.

Idan dai ba a manta ba, shugaban ƙungiyar AIRLIN na Ƙasa, Alhaji Muhammad Gamawa ne ya ƙaddamar da ƙungiyar AIRLIN na Jihar Nasarawa a ranar Asabar a cibiyar ’yan jarida ta NUJ da ke Lafiya.

By ukarofi