Daga MAHDI M. MUHAMMD
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta koka da yadda rashin tsaro, talauci da jahilci ke jefa yankin Arewa cikin matsaloli.
A jawabinsa na ranar Litinin a Kaduna, yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Uba Sani a gidan Sir Kashim Ibrahim, shugaban ƙungiyar ACF, Mamman Mike Usman ya buƙaci shugabanni da al’ummar yankin da su gaggauta sauya tunani da tsare-tsare marasa kyau ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugaban ACF ya ce; “A cikin ƙoƙarinmu, da shugabannin Arewa, da suka haɗa da gwamnonin jihohi, sarakuna, da sauran dattawa, sun yanke shawarar kafa ACF a shekarar 2000. Saboda bada shawarwari ta yadda za a kawar da irin wannan matsalar ta tsaro da rigingimu a yankin.
“Manufar ita ce, a haɗa kai a zama ɗaya wajen wakiltar al’ummomin Arewacin Nijeriya ba tare da la’akari da siyasa, ƙabilanci, ko addini ba. ACF ita ce ta yi aiki a matsayin Majalisar Jama’a ko Dattawa wacce ta buɗe idanu da kunnuwa don yin la’akari da al’amura da ci gaban da ka iya haifar da rashin jituwa, ko rikici a faɗin Arewa da bunƙasa ci gaban yankin.
“A yau, duk da jajircewar da muka yi, samun zaman lafiya da haɗin kai da ci gaba a Arewa, lamari ne da dole sai an jajirce wajen ƙoƙarin gudanar shi. Duk alƙaluman da ke nuna koma baya a ci gaban bil’adama, talauci, jahilci, da rashin tsaro na rayuka da dukiyoyi, sun jefa Arewa a cikin rami mai zurfi, lallai akwai babban aiki da ke jiran duk ’yan Arewa.”
A cewarsa, ACF ta himmatu wajen bayyanawa da kare muradun al’ummar Arewa ta hanyar ayyukansu daban-daban.
“Ɗaya daga cikin irin ayyukan ƙungiyar shi ne, kwamitin fasaha da aka kafa kwanan nan wanda ya sake nazarin kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Rahoton kwamitin ya haɗa alaƙar ACF da kwamitocin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta ƙasa kan sake duba kundin tsarin mulki. Ba da jimawa ba, za a gabatar da rahoton kwamitin fasaha na ACF ga ƙungiyar gwamnonin Arewa,” inji Usman.
