
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin Oando ya kammala sayan kamfanin ‘Nigerian Agip Oil Company’ (NAOC) akan Dala miliyan 783.
Kamfanin ya bada sanarwar ne a ranar Alhamis ta ofishin Satarensa, Ayotola Jagun inda ya ce hakan ya nuna cewa Oando ya zama mallakin NAOC ɗari-bisa-ɗari daga kamfanin Eni na ƙasar Italiya.
Haka nan, wannan wani cigaba ne ga Oando kasancewar sa ɗaya daga kamfanonin da ke taka muhimmiyar rawa a ɓangaren samar da man fetur da gas a Najeriya.
Sannan, cigaban zai taimaka wajen ƙara mamaye kaso mai tsoka a kasuwancin haɗaka da sauran kamfanoni da kuma faɗaɗa sakamakon da rijiyoyin gas ke bayar wa.
Shugaban kamfanin Oando, Wale Tinubu ya ce sanarwar, manufa ce da su ke ta ƙoƙarin cimma tsawon shekaru goma tun lokacin da suka ƙulla haɗakar kasuwancin a shekarar 2014 ta hanyar mallakar ‘Conoco Phillips Nigeria Portpholio’.
Ya kuma ce, wannan nasara ce ga Oando da dukkan takwarorinsa yayin da ake fatan hakan ya zama sababin inganta harkokin kamfanin.
