Obasanjo ya musanta hannu a ƙudurin da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas suka dauka kan Nnamdi Kanu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce ba a kan batun sakin Nnamdi Kanu suka tattauna ba a lokacin da ya gana da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas a ranar Talata.

Gwamnoni a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas sun yanke shawarar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan sakin Kanu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar ƙasar Biafra (IPOB).

Hope Uzodimma, gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar, ya bayyana shirin “tattaunawa” da gwamnatin tarayya kan Kanu a matsayin ɗaya daga cikin ƙudurorin da aka cimma a taron Enugu.

Obasanjo ya kuma kai ziyarar haɗin kai a taron gwamnonin Kudu maso Gabas a ranar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Kehinde Akinyemi, mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Obasanjo ya ce ganawar da ya yi da gwamnonin ta ta’allaƙa ne kan “batun ci gaban yankin”.

“Batun ci gaban yankin sun haɗa da na tsaro da ababen more rayuwa. Sauran sun kasance na tattalin arziki da haɗin guiwa wanda aka yi niyya don dacewa da ajandar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa,” inji sanarwar.

“Ganawar da su ta kasance bisa gayyata ta da kuma na Cif Emeka Anyaoku kafin a fara taron nasu. Batun Nnamdi Kanu ba ya cikin ajandar, kuma ba a tattauna a gabana ba,” inji Obasanjo.

Kanu dai yana hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan da aka tasa ƙeyar sa zuwa Nijeriya a shekarar 2021. Ana tuhumar Kanu bisa zarginsa da laifin cin amanar ƙasa kuma an hana shi beli a watan Mayu.

By ukarofi