Daga USMAN KAROFI
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaɓen 2027 mai zuwa.
An bayyana hakan ne a ranar Asabar jim kaɗan bayan jam’iyyar NDC ta tabbatar da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a taronta na musamman da aka gudanar a Abuja. Wannan mataki ya tabbatar da jita-jitar da ta daɗe tana yawo kan yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu.
Obi ya fito ne a matsayin dan takara ɗaya tilo a jam’iyyar, sannan aka miƙa masa tutar jam’iyya a gaban shugabannin NDC da wakilan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Masu sharhi kan siyasa na ganin wannan haɗaka tsakanin Obi da Kwankwaso na iya canza lissafin siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027, kasancewar kowannensu yana da karfin tasiri a ɓangarori daban-daban na ƙasar.
Ana ganin Obi na da goyon baya mai yawa daga matasa da mazauna birane musamman a Kudu maso Gabas da wasu sassan Kudu maso Kudu, yayin da Kwankwaso ke da tasiri sosai a Arewa musamman jihar Kano ta hannun tafiyar Kwankwasiyya.
Haɗin kan su ya biyo bayan ficewar su daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sakamakon rikice-rikicen cikin gida, lamarin da ya kai su shiga NDC domin neman sabon dandali na siyasa kafin zaɓen 2027.
