Odeh da Adewunmi sun zama jagororin yaɗa labarai a NNPC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya sanar da naɗin ƙwararru biyu, wato Andy Odeh da Misis Morenike Adewunmi a wasu manyan muƙamai da nufin inganta harkokinsa.

An naɗa Odeh ne a matsayin Shugaban harkokin yaɗa labarai yayin da Misis Adewunmi kuma ta zama babbar jami’ar hulɗa domin gudanar da ɓangaren hulɗa da jama’a da samar da dabarun gudanarwar harkokin masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran Andy Odeh, wanda ke da ƙwarewa na tsawon sama da shekaru talatin a fannonin sadarwa, talla da masana’antar mai da gas, zai bada gagarumar gudumawa ga harkar sadarwa a kamfanin.

Gabanin fara aiki da NNPC, Odeh ya shafe tsawon shekaru 26 yana aiki da kamfanin makamashi na ‘Nigeria LNG’ inda ya riƙe muƙamai da dama masu alaƙa da hulɗa da jama’a da ci-gaba mai ɗorewa a fannonin fasaha da dai sauransu.

A ɗaya gefen kuma, Adewunmi, wadda ta kasance lauya mai ƙwarewar sama da shekaru 25 a fannin albarkatun mai, ta koma aiki ne a NNPC daga kamfanin ‘Shell Companies in Nigeria’, inda ta ƙware a fannonin gudanarwa, hulɗa da gwamnati da gudanarwar lamuran masu ruwa da tsaki.

By Babaji