Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta yabawa kamfanonin mai na NNPC/SHELL da suka samu tallafin karatu ga ɗalibai uku masu hazaƙa a Jihar Zamfara domin yin karatu a jihar Neja tun daga ƙanana zuwa babbar sakandare.
Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha, Alh Wadatau Madawaki yayi yabon a lokacin da yake gabatar da ɗaliban huɗu ga manema labarai .
Kwamishinan ya jaddada shirin gwamnatin jihar da kuma jajircewa ta wajen samar da duk wasu hanyoyin da za su inganta ilimi mai inganci, musamman kan tsarin ilimin yara mata.
“Wadannan ɗalibai guda huɗu da kamfanonin NNPC/SHELL suka ɗauki nauyin karatunsu, za su yi karatu har zuwa matakin SS3 a ƙarƙashin shirin NNPC/SHELL na bayar da tallafin karatu”.
Kwamishinan, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatarsa ta samu dalibai 567 da suka gama jarabawar Firamare waɗanda 540 daga cikin su suka ci jarrabawar da mafi kyaun maki.
Ya ce dukkanin ɗaliban 540 gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin karatunsu a makarantun haɗin kai da ke jihohin Sokoto da Zamfara watau Unity Schools).
“Gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an inganta ilimin ‘ya’ya mata, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimin boko har zuwa matakin SS3.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta shirya don sake buɗe makarantun kwana guda tara a Gummi, Mafara, Gusau, Shinkafi da Ƙaura Namoda.
Ya kuma buƙaci iyaye da su riƙa tallafa wa ‘ya’yansu domin a sa su makaranta don samun al’umma ta gari.
