Tinubu ya umarci a ƙara ƙarfafa tsaro a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin ne bayan wata ganawa da Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa tare da tawaga mai ƙarfi da suka je neman agajin gaggawa daga gwamnatin tarayya kan taɓarɓarewar tsaro a jihar.

Ya kuma umurci hukumomin tsaro da su sake duba dabarunsu tare da ƙara tura jiragen leƙen asiri na sama, sannan ya amince a sake rarraba sojoji tsakanin Katsina da sauran iyakokin da ke makwabtaka don yaƙar ’yan ta’adda kai tsaye.

“Yau, na umarci hukumomin tsaro su ƙara kuzari, da sake duba dabarun da ake amfani da su.

Za a tura ƙarin jiragen leƙen asiri, kuma idan akwai buƙatar su matsar da sojoji daga Katsina zuwa iyakokin maƙwabta, su yi hakan. Kuma za su kawo mini rahoto nan take,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban Ƙasan ya bayyana girman ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, inda ya ce: “Abin da ke faruwa a ƙasar nan na ƙalubalen tsaro da muke fama da shi ba ƙarami ba ne. Haƙiƙa iyakokinmu sun yi rauni. Mun gada da wannan rauni, amma ƙalubale ne da dole mu fuskanta, kuma muna fuskantarsa.”

Shugaban ƙasa ya tabbatar tawagar cewa sojojin ƙasa za su ƙara matsa ƙaimi wajen kawar da miyagu, inda ya yi alƙawari: “Sojojin ƙasa suna nan. Za mu ci gaba da kai masu hari a maɓoyarsu.”

Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin wani ɓangare na cikakken tsarin magance matsalar tsaro.

“Dole mu kare ’ya’yanmu, al’ummarmu, hanyoyin rayuwarmu, wuraren ibada da wuraren nishaɗinmu. Ba za su tsoratar da mu ba,” in ji shugaban ƙasa.

A nasa jawabin Gwamna Dikko Radda ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa manufofinsa na buɗe ƙofa da kuma goyon bayan da ba ya gushewa ga Jihar Katsina, inda ya ce duk wata buƙata da aka gabatar masa kullum yana amincewa.

“Shugaban Ƙasa ya nuna kansa a matsayin ɗan Katsina na gaskiya. Mun kasance masu godiya kan yadda yake nuna damuwa kan matsalolin tsaronmu,” in ji Gwamna Radda.

Tun da farko a jawabin sa na bude taro, Sarkin Katsina, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida ya wakilta, ya roƙi Shugaban Ƙasa da ya ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro tare da kafa bataliya ta soja da kuma rundunar ’yan sandan MOPOL a kudancin Katsina.

Ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta kashe sama da Naira biliyan 40 wajen bayar da tallafin kayan aiki da goyon bayan tsaro ga hukumomin tarayya duk da ƙarancin kuɗaɗen jihar, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta mayar da wani ɓangare da kuma taimakawa waɗanda abin ya shafa.

Tawagar ta haɗa da mataimakin gwamna na Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Joɓe; Kakakin Majalisar Dokokin, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; tsohon Gwamna Aminu Bello Masari; Sanatocin Katsina guda uku; da ’yan Majalisar Tarayya daga jihar.

Haka kuma a cikin tawagar akwai Injiniya Ahmed Musa Dangiwa, Ministan Gidaje; da Barista Hannatu Musa Musawa, Ministar Harkokin Al’adu da Ƙere-ƙere.

Sauran sun haɗa da Hajiya Hadiza Bala Usman, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Tsare-tsare da Daidaito; Jabiru Salisu Tsauri, Kwamishinan AUDA-NEPAD na Ƙasa; mambobin Majalisar Zartarwa ta Katsina; Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Faruq Umar; Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah); Alhaji Tukur Jikamshi tsohon mataimakin gwamna; Malam Gambo, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina; da hamshaqin ɗan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Wannan taron na cikin jerin muhimman matakai na ƙarshe domin kawo ƙarshen ta’addanci da ’yan bindiga ke yi wa al’ummar Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

By ukarofi