Okonjo-Iweala ta maida martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi vame da cire Tinubu a hotonta

Daga BASHIR ISAH

Shugabar Cibiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta maida martani bayan da wasu ‘yan Nijeriya suka yi ca a kanta saboda cire Shugaba BoIa Tinubu da ta yi a wani hoton da suka ɗauka a wajen babban taron da ya gudana a Paris, babban birnin Faransa kwanan nan.

A ranar Juma’a aka ga Okonjo-Iweala ta waIIafa hoton da suka ɗauka a wajen taro a shafinta na Tiwita inda a ciki aka gano ta yanke inda ya kamata a ga Shugaba Tinubu.

Tinubu na daga cikin mahalarta taron wanda Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya shirya.

Taron ya bai wa Shugaba Tinubu damar bayyana burinsa a idon duniya na neman a ƙarfafa tattalin arzikin Afirka da kuma buƙatar da ke akwai na gaggauta daƙile matsalar talaucin da ke addabar yankin haɗi da matsalar sauyin yanayi.

Cire Tinubu a hoton ya haifar da zazzafar muhawara musamman ma a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC da na Peter Obi.

Sai dai a martanin da ta yi kan batun wanda ta wallafa a shafinta na Tiwita a ranar Asabar, Okonjo-Iweala ta ce ce-ce-ku-cen da ɓangarorin biyu ke yi ya nuna ƙarfin rabuwar kawuna da ake fama da shi a Nijeriya

Ta ce takan wallafa hotuna ne yadda ‘yan rakiya ko ma’aikata suka miƙa mata, zurfafawa wajen bai wa hoton ma’ana ta badan ba daidai ba ne.

“Mu haɗa kai wajen gina ƙasarmu amma ba mu farmaki juna ba,” in ji Okonjo-Iweala kamar yadda ta wallafa a shafinta na Tiwita.