Ondo: Kotu ta bai wa ‘yan sanda umarnin biyan diyyar milyan N100 ga tsohon mataimakin gwamna

Daga WAKILINMU

Wata Babbar Kotu mai zamanta a Akure babban birnin jihar Ondo, ta umarci rundunar ‘yan sandan jihar da ta biya diyyar Naira milyan N100 ga Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Agboola Ajayi.

Laifin da ya haifar wa ‘yan sandan hukuncin biyan diyyar shi ne, a ranar 20, Yuni, 2020 ‘yan sandan sun hana mataimakin gwamnan jihar na wancan lokaci, wato Agboola Jayi, fita daga Fadar Gwamnatin jihar wajajen ƙarfe 7 na dare, haka ma abin ya sake faruwa washe gari 21, Yuni, 2020 da misalin ƙarfe 9 na safe, bisa zargin cewa Ajayi na take-taken ficewa daga jam’iyyar APC.

Bayan dogon nazari, alƙalin kotun Jastis F. A. Olubanjo, ya ɗauki halin da jami’an tsaron suka nuna a matsayin rashin martaba doka da kuma damar ‘yancin zirga-zirga da kundin tsarin mulki ya bai wa ‘yan ƙasa da sauransu.

Alƙali Olubanjo wanda ya yanke hukuncin biyan diyyar milyan N100 kan ‘yan sandan, ya ce muddin ‘yan sanda suka iya aikata wannan hali ga Mataimakin Gwamna mai ci wanda ke sanye da rigar kariya ta mulki, ashe kenan wata rana za su iya sace Shugaban Ƙasa sannan su fake da cewa bincike suke gudanarwa.

Shari’ar, mai lamba FHC/AKCS46/2020 ta gudana ne kan take ‘yancin Tsohon Mataimakin Gwamanan da aka yi wanda lauyan Agboola, Babs Akinwunmi, ya shigar da ƙara gaban kotu.

Tun da farko, an shigar da ƙarar ce a Abuja amma daga bisani Alƙali Okon Abang ya ɗage ta zuwa Akure a bisa dalili na hurumin sauraron shari’a.

Waɗanda shari’ar ta taɓo su, su ne; Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP), Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ondo, Babban Darakatan DSS, DSS kanta da kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ondo.