Daga MAHDI M. MUHAMMAD
ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ce, ƙarin farashin man fetur a Nijeriya ya haifar da fargaba, inda da yawa ke nuna yatsa tsakanin masu samar da man, musamman ma matatar man Dangote da Kamfanin NNPC.
Sai dai babban Sakataren OPEC, Haitham Al Ghais, ya bayyana cewa, ainihin dalilan da ke haddasa hauhawar farashin man fetur, sun ta’allaƙa ne a abubuwa da dama, musamman a irin harajin da gwamnatoci ke sanyawa, ciki har da na manyan ƙasashe masu man fetur.
A wani rubutu da aka wallafa a ranar Talata, Al Ghais ya bayyana cewa ɗanyen mai da sauran abubuwan da ake amfani da su shi ne kashin bayan masana’antun duniya, wanda ke da ƙarfin komai tun daga sufuri zuwa wadatar da mai.
Yayin da wasu da dama ke ganin cewa hauhawar farashin man fetur na amfanar masu haƙo mai ne kai tsaye, inda yake ƙarewa a kan al’umma, shugaban ƙungiyar ta OPEC ya ƙaryata wannan zargi, inda ya yi nuni da cewa ƙasashen da ke haƙo mai ba su ne kan gaba wajen cin gajiyar sayar da mai ba.
Tsakanin 2019 da 2023, ƙasashen maau haƙo man fetur sun sami kusan dala tiriliyan 1.915 a duk shekara fiye da ƙasashen OPEC daga kayayyakin mai.
A cikin 2023 kaɗai, haraji ya kai kusan kashi 44% na farashin dillalan man fetur na ƙarshe a ƙasashen OECD, kuma a wasu ƙasashen Turai, wannan adadi ya zarce kashi 50%.
