Osinbajo ya musanta alaƙarsa da ginin da ya rushe a Legas

Daga AISHA ASAS

Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ya ƙaryata zargin alaƙarsa da gini mai hawa 12 wanda ya ruguje a Ikoyi da ke cikin birnin Legas.

Farfesa Osinbajo ya bayyana cewar, ba shi da alaƙa ko ra’ayi na mallakar wannan dogon ginin da ya rushe. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jajanta wa mutane kan lamarin.

A wata sanarwar da ta fito ta hannun Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mr. Laolu Akande a nan Abuja, Osinbajo ya jajanta wa iyalai da ‘yan’uwan waɗanda suka mutu da waɗanda suka ji rauni a wannan iftila’in. Ya kuma bayyana matuƙar damuwarsa akan faruwan wannan al’amari.

Mr. Laolu ya ƙara da cewa, mataimakin shugaban ƙasa ya yi baƙin ciki kan alaƙanta shi da wannan wuri da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama. wanda sananniyar kafar yaɗa labarai ta yanar gizo ta yi.

A rahoton wannan kafar ta yaɗa labarai, ta bayyana mataimakin shugaban ƙasa a matsayin mamallakin filin da aka yi wannan gini, wanda ya siya daga hannun Chief Michael Ade-Ojo, shugaban kamfanin motoci na ‘Elizade Motors’. Haka zalika kafar ta sanya kanta a yaƙin neman rufe ginin.

A cewarsa, “Ina mai tabbatar wa jama’a cewa Farfesa Yami bai sayi filin da aka yi wannan ginin ba, kuma ba hannunsa a gina wannan filin.” Ya ƙara da cewa, “Mataimakin shugaban ƙasa bai taɓa siyan wani fili ba tun bayan hawansa mulki.”

Haka nan, ya ƙaryata zargin na alaƙa ta cinikayya da ke tsakanin Osinbajo da Chief Michael Ade-Ojo, inda yake cewa, “Farfesa Yami bai siye wannan fili ba, asali ma ba wata alaƙa ta cinikayya da ta taɓa shiga tsakanin mataimakin shugaban ƙasa da Chief Michael.”

Akande ya ƙara da musanta zargin sa hannun mataimakin na shugaban ƙasa a buɗe wannan aikin na gini tare da ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu. “

Mai Magana da yawun Osinbajo ya shaida wa manema labarai cewa, duk wata ƙaddara da Farfesa Yami ya mallaka sananniya ce ga al’ummar Nijeriya, domin an bayyana su a baina jama’a kafin hawansa mulki, ya kuma tabbatar da cewa har yau ba abin da ya ƙaru daga ƙaddarorin da ya mallaka.

“Na yi mamakin wannan mugunta ta waɗanda ke amfani da ƙunci da baƙin cikin mutane wurin yaɗa ƙarya don biyan buƙatarsu.” Cewar Mr. Laolu.

Ya ci gaba da cewa, “Mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan iftila’in, wanda ya kamata a taya su alhini, sai dai wasu na amfani da zafin rashin da suka yi don cimma wata manufa ta siyasa.

“Babu shakka waɗanda ke da hannu a ƙyanƙyashe wannan gurɓatacen labarin za a biya su jingar aikin nasu.” Inji shi.

Mr. Laolu Akande ya tabbatar da cewa ba za a samu sanannu da kuma ƙwararrun ‘yan jarida a cikin waɗannan masu yaɗa ƙarya don samun biyan buƙata ba, domin ƙwararren ɗan jarida ba ya amfani da saninsa wajen faranta ran wani ɓangare.

Daga ƙarshe ya bayyana cewar mataimakin shugaban ƙasa ya miƙa wannan al’amari ga lauyansa don bin hanyoyin da suka dace na ganin an wanke shi tare kuma da ɗaukar mataki kan waɗanda suka jefi shi da wannan zargin daidai da dokokin ƙasa.