
Daga BELLO A. BABAJI
Al’amarin tsaro ya samu tsaiko a gidan gyaran hali na Ilesa dake Jihar Osun, sakamakon iska mai ƙarfi yayin mamakon ruwan sama da ta yi sanadin ruftawar wani sashe na gininsa, lamarin da ya taimaka wa fursunoni bakwai tserewa.
Jami’an Hukumar kula da Gidajen Yari (NCoS), sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Waɗanda suka tseren sun haɗa da John Michael mai shekaru 34; Tobi Akin ɗan shekara 19; Eze Nweze ɗan shekara 40; Olalekan Ajofoyinbo mai shekaru 45; Ninalowo Yusuf, shekaru 28; Matthew Ogunjimi mai shekaru 20 da kuma Kabiru Oyedun mai shekaru 39.
An sanya ladar Naira miliyan 5 ga kowane ɗaya daga cikin fursunonin da wani ko wasu suka taimaka aka kamo.
Rahotanni sun bayyana cewa, an tsaurara matakan tsaro a gidan yarin da kewayensa a daren ranar Laraba.
Kakakin hukumar a Osun, Joel Oyedokun ya tabbatar da cewa tuni aka baza jami’an tsaro a yankin kurkukun gami da mayar da cibiyarsu zuwa Ilesa domin farauto waɗanda suka tsere.
Ya kuma ce, jami’an sojoji da na DSS suna aiki tare da su wajen ganin an cimma nasarar dawo da fursunonin gidan gyaran halin.
