Sirrin kyau da lafiya: Hanyoyi 12 da za su samar da kyakkyawar fata, da gashi (2)

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

6. Yin amfani da lalle:

Lalle na ɗauke da sinadaran da ke tsaftace fata, yana kuma hana kuraje.

Shawara: Zai fi kyau a fara shafa lallen a hannu, ga wanda bai taɓa yi ba, kafin a shafa gabaɗaya, don sanin ko naki jikin na karɓar shi, domin gujewa allergy.

7. Kwalliya mai sauƙi da tsafta:

Wani abu da mata ba su sani ba, kwalliya mai sauƙi, kamar hoda, turare da jan baki, ma’ana kwalliyar da ba a yi mata shafe-shafe mai yawa ba a mafiyawan lokuta ya fi kyau da rashin illa ga ga lafiyar fata. Amma fa kayan kwalliya masu tsafta da inganci ne kawai ya kamata a yi amfani da su.

Shawara: Kada a yi barci da kwalliya a fuska, domin yana rufe ramukan fata (pores) yana jawo kuraje.

8. Shiga ta mutunci:

Wasu suna tsammanin a iya kare mutunci kawai suturta jiki ya tsaya, saidai abinda ba su sani ba, saka hijabi da tufafin kamala ba wai kare tarbiyya kawai suke ba, suna kuma kare fata daga rana da ƙura.

Bincike ya nuna, hasken rana mai ƙarfi (UV rays) na janyo tabo, baƙi, da saurin tsufa a fata. Hijabi na hana wannan (Skincare and Sun Protection Guide, 2022).

9. Barci isasshe:

Rashin barci yana haddasa kumburin ido, fata mai duhu, da rashin kuzari. Masana sun nuna mace na buƙatar barci na sa’o’i 7 zuwa 8 a kowace rana.

Shawara: Ki rage amfani da wayar hannu kafin barci domin hakan na hana ki saurin barci, kuma hakan na nufin shiga tsakanin ki da hutu.

10. Lafiyar zuciya da kyawon fuska:

Macen da ke tare da farin ciki a zuciyarta na bayyana a fatarta ta hanyar sheƙi, fiye da wadda ke cikin damuwa. Damuwa tana sa gashi ya zube, fata ta bushe, da fuska ta yi ja. Wato dai farin ciki kawai wata hanya ce ta gyaran fata.

Binciken American Psychological Association (APA) ya nuna cewa, stress na rage sinadaran kariya a fata.

11. Halaye masu kyau:

Mace mai haƙuri, tausayi da karamci, wato mai kyakkyawan hali, wanda ya fi kyaun fuska da dukka jiki.

kyakyawan hali na sa mutane kallonki da yadda zuciuarki ta ke, wato mai kyau, tuna da yadda ba wai yadda ki ke kallon kanki a madubi ba.

12. ƙwarin gwiwa da ƙaunar kai:

Sau da yawa yadda muka ɗauki kanmu ne kyawonmu, wanda hakan ke sa a duk lokacin da iyaye ko miji ga matarsa ya kasance suna yawan faɗar ba ki da kyau, to za a waye gari ki aminta da ke ba mai kyau ba ce, kuma ko duniya za ta taru ta sanar da ke kina da kyau ba za ki yarda ba. Don haka son kai a wannan ɓangaren yana da kyau. Ki riƙa yaba kanki. 

Ga macen da ta taso iyaye ko miji na kushe kamarta ko kyanta, ki tabbatar kina yaƙar kalaman nasu a zuciyarki. Ki yawaita maimaitawa kanki cewa, “Ni mace ce mai daraja, kuma ina da kyau.”

Daga ƙarshe, kada ki bar duniya ta canza miki tunani. Kyau ba na Instagram ko TikTok kaɗai ba ne, domin da yawa ana kushe su ne don ba babu masaniyar abinda suke yare da shi, domin ahi kyau yana cikinki ne ba wajenki ba.

Kyau ba abu ne guda ɗaya ba. Kyau shi ne, lafiya, tsafta, da hali. Kyau kan iya zama na fatar jikinki, da zuciyarki mai tsafta.

By ukarofi