Shin shan zaƙi na ƙara ciwon basir?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Manhaja. A wannan makon, za mu ɗauki wani ɓangare daga cutar basir, domin kamar yadda ku ka sani, shafin Iyali na taɓo kowane ɓangare, matuƙar ya shafi iyali.

Basir wata cuta ce da ke addabar dubura, tana haifar da ciwo, ƙaiƙayi, a wani lokaci kuwa akan iya samun zubar jini. Ciwon basir kusan in ce ya zama ruwan dare, har wasu ke ganin shi ba koamai ba idan ka cire ciwon da yake haifarwa, saidai abinda ba su sani ba, illarshi mai yawa ce.

Yayin da mutane da dama ke neman sauƙi daga wannan ciwo, ana yawan tambaya ko shan zaƙi, kamar lemon kwalba, cakulan, da alewa na da hannu wajen tsananta cutar. Wannan tambaya na da muhimmanci musamman a Arewacin Najeriya, inda shan kayan zaƙi ya karu sosai, musamman tsakanin matasa da yara.

Masana sun tabbatar da cewa, shan zaƙi wanda ba lallai ne shi kaɗai ne ya haddasa basir ba, amma yana da tasiri wajen ƙara tsananta shi. Shan lemo da sauran kayan zaƙi na iya haifar da:

Rashin ruwa a jiki (dehydration) wanda ke sa bayan gida ya daskare. Kuma kamar yadda wani darasi da muka yi a baya muka bayyana yadda rashin ruwa a jiki ke haddasa matsaloli ga jiki da ka iya kai ga ababe da dama, kamar suma, jijigar jiki da sauran su.

Kumburin ciki da ƙarin ƙiba wanda ke ƙara matsin lamba a dubura. Duk da cewa har yau wasu ba su aminta cewa, kayan zaƙi na ƙara ƙiba ba, kuma ba za ka ja da su ba, domin ba kowane kayan zaƙi ne ke haifar da ƙiba ba.

ƙarancin fiber a jiki.

Kamar yadda aka sani, daga cikin ayyukan sinadarin fiber akwai sawwaƙa bayan gida, wanda kamar yadda muka sani, yawan yunƙuri yayin da aka je bayan gida na daga cikin abinda ke haifar da basir musamman mai tsiro, kuma kayan zaƙi ba a cika samun sinadarin fiber ba, wanda ke sauƙaƙa bayan gida.

Waɗannan dalilai kan janyo yunƙuri da ƙarfi yayin bayan gida, wanda shi ne babban abinda ke haddasa ciwon basir ko kuma tsananta shi.

Shawarwari ga masu fama da basir:

1. Rage yawan shan lemo, cakulan, da alewa.

2. Sha ruwa mai yawa – aƙalla gilashi takwas a rana.

3. Cin abinci mai ganye da fiber, kamar kabeji, doya, ayaba, dambu da alkama.

4. Guji tsayuwa ko zama na dogon lokaci ba tare da motsi ba.

5. A dinga amfani da ruwa mai dumi domin wanke dubura ko zama a ciki (sitz bath).

Daga ƙarshe, shan kayan zaƙi ka iya zama abin jin daɗin rai, amma ga masu fama da basir, yana iya janyo ƙarin ciwo da kafiyar ciwon ta hanyar rashin jin magani. Don haka, lafiyar dubura na buƙatar kulawa daga abincin da muke ci. Yin sauye-sauye a abinci na iya rage ciwon da hana sake kamuwa da cutar bayan an warke daga gare ta.

By ukarofi