Yanzu-yanzu: Tinubu ya aike da kasafin tiriliyan N1.48 na Ribas ga majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu ya aika kasafin Naira tiriliyan 1.48 na Gwamnatin Jihar Ribas ga majalisar dokoki domin gudanar da aiki akansa.

Tinubu ya ce, hakan abu ne da ke da muhimmanci duba da hukuncin Kotun Koli na soke kasafin 2025 na jihar da kuma halin dokar ta-ɓaci da take ciki a yanzu.

Ya kuma ce, ₦324bn daga ciki za a yi amfani da shi ne wajen aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa, ₦166bn ga ɓangaren lafiya, yayin da ₦75.6bn kuma za a sanya shi a ilimi, sannan ₦31.4bn ga harkar noma.

Ya ƙara da cewa, ɓangaren noma a kasafin zai taimaka wajen samar da guraben ayyuka guda 6,000, lamarin da ya sa ya roƙi majalisar da ta gaggauta kammala aiki akan kasafin domin amfanin jihar da al’ummarta.

By Babaji