
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa adawa PDP, ta yi alla-wadai da fashewar bom a wani masallacin Maidugurin Jihar Borno, wanda ya auku ana tsaka da sallar Magriba a yammacin ranar Laraba, tana mai bayyana al’amarin a matsayin abin takaici da ba za ta lamunta ba.
A wata takarda da ta aike wa manema labarai ta hannun Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ini Emembong, PDP ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza wajen bada kariya ga rayuka da dukiyoyin ƴan Nijeriya.
“Labarin fashewar bom a wani masallacin kasuwar Gamboru, Maiduguri, wani abin baƙin ciki ne da ke sake tunatar da yadda al’amarin rashin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa da al’ummar Nijeriya ke fuskanta”, inji sanarwar.
Jam’iyyar ta kuma jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu yayin harin, tana mai jimamin rasuwa a lokacin da mutum yake tsaka da bauta wa mahaliccinsa.
PDP ta kuma yi gargaɗin matuƙar aka cigaba da barin hare-haren a wuraren bauta ba tare da bincike da ɗaukar matakan da suakdace akansu ba, hakan ba zai kaɗai zama karya dokokin ƴancin ƴan ƙasa ba, har ma zai iya zama barazana da jefa tsoro acikin al’umma a lokacin ibada.
Don haka ne ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihar ta su gaggauta ɗaukar matakin bada kariya ga rauykan al’umma a yayin bukukuwan ƙarshen shekara da nan gaba.
Kakakin rundunar ƴan sandan Borno, ASP Nahum Daso ya shaida wa manema labarai cewa mutane 5 ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da guda 35 suka jikkata.
