Raɗɗa ya karɓi shaidar lashe zaɓen gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, ta ba wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa takardar shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar a ranar Alhamis.

Kwamishinan hukumar zave mai wakiltar Jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Farfesa A. A Zuru ne ya miƙa shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisar dokoki na jihar su 31.

Da yake jawabi, Dr. Dikko Raɗɗa, ya gode wa Allah bisa nasarar da ya samu na lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023.

Ya kuma yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, duba da yadda ta gudanar da ingantaccen zaɓe wanda a cewarsa ba a taɓa gudanar da irinsa ba a tarihin siyasar Nijeriya.

Daga nan ya sha alwashin gwamnatinsa za ta yi tafiya da kowa, gami da neman ra’ayin al’umar jihar kafin zartar da manyan aikace-aikacen gwamnati a jihar.

Tun farko da yake jawabi, Shugaban hukumar zaɓe na jihar, Farfesa Yahya Maƙarfi Ibrahim, ya bayyana cewar bada takardar shaidar cin zaɓen doka ce da hukumar ta ayyana cewar za a miƙa ga zaɓaɓɓun ‘yan takara cikin kwanaki 14 bayan an bayyana su a matsayin waɗanda suka yi nasara.

Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, na daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron wanda ya gudana a hedikwatar Hukumar ta INEC reshen jihar Katsina.