Kano: Abba Kabir ya naɗa Sanusi Bature matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labarai

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa fitaccen ɗan jaridar nan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labaran sa.

Naɗin na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamitin sabon gwamnan ya fitar a ranar Alhamis a madadin zaɓaɓɓen gwamnan.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya bayyana Sanusi Bature Dawakin Tofa a matsayin wanda ya cancanta sakamakon ƙwazonsa, haƙuri da kuma biyayya.

Dawakin Tofa wanda ya kasance fitaccen ɗan jarida mai ƙwarewar aiki ta shekaru 19 a fagen aikin jarida, kuma yana cikin masu bada gudunmuwa mai girma a Jihar Kano da ƙasa har ma da ƙasashen ƙetare.

Kuma shi ne wanda ya yi nasarar lashe shaidar karramawa a shekara ta 2008 a fannin binciken harkokin ilimi, inda kuma ya yi aiki a fanni daban-daban a ciki da wajen ƙasar nan, kama daga ofishin British Foreign & Commonwealth Development (FCDO) da sauransu.

Kazalika, ya riƙe muƙamai da dama kama daga manajan bai ɗaya na sashen samar da abinci na kamfanin Ɗantata, Darakta a YieldWise, Manajan shirye-shirye na Girl Rising ƙarƙashin kulawar Amurka da dauransu.

Ya samu shaidar kammala karatun digirinsa na na farko (B.A Hons.) a ɓangaren aikin jarida daga Jami’ar Maiduguri, yana kuma da shaidar karatu ta HND, PGD da sauransu.

Ya halarci kwasa-kwasai masu tarin yawa a ciki da eajen Nijeriya.

Kafin dabon naɗin nasa, shi ne Mataimakin Shugaban kamfanin Kingston organic PLC da ke kasar ingila.