Shugaban Man City ya zama mataimakin shugaban Daular Larabawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta naɗa mamallakin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City da ke Ingila, Sheikh Mansour bin Zayed a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Ƙasar.

A cikin wata sanarwa da Kamfannin Dillancin Labaran ƙasar na Wam ya wallafa, ƙasar ta ce attajirin ya ɗare kujerar ce a matsainsa na shugaban gwamnati.

Shugaban Ƙasar ne dai ya sanar da amicewar naɗin, inda ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Ƙolin Ƙasar na naza Sheikh Mansour a matsayin.

Kafin naɗin nasa dai, attajirin shi ne Mataimakin Fira Ministan ƙasar.

Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya ayyana sunan ɗansa, Sheikh Khaled bin Mohamed bin Zayed, a matsayin Yarima mai jiran gadon Abu Dhabi, wacce ita ce masarauta mafi arziki a jerin masarautun ƙasar bakwai.

Hakan dai na nufin dan nasa shi ne zai kasance mai jiran gadon sarautar ƙasar bayan mahaifinsa.

Shiekh Mansuor dai ya tava zama Mataimakin Fira Minista kuma Shugaban kotun ƙasar, tare da rike wasu gwababan mukamai musamman a ɓangaren kasuwanci.

A watan Mayun bara ne dai aka ayyana Sheikh Mohamed bin Zayed a matsayin Shugaban Ƙasa bayan rasuwar ɗan uwansa, Sheikh Khalifa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *