‘Yan bindiga sun kashe jaririn da aka haifa a wajensu, sun saki mahaifiyarsa a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wata mata mai juna biyu a Ƙaramar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna sun sake ta bayan sun kashe jaririn da ta haifa a sansaninsu.

Rahotanni sun ce maharan sun saki matar ce mai suna Shamsiyya Mustapha, wacce aka sace tare da mijinta da kuma ’yarsu mai shekara 16 a ƙauyen Janjala da ke Ƙaramar Hukumar ta Kagarko, ranar 5 ga watan Fabrairu.

Sai dai daga bisani maharan sun saki mijin matar bayan karɓar kuɗin fansa Naira miliyan biyu da sabon babur da kayan abinci, amma suka ci gaba da riƙe matar da ’yar tasu har sai an ƙara musu wata miliyan biyun.

Da yake tabbatar da lamarin ta wayar salula ga wakilinmu, ɗaya daga cikin ’yan uwan matar, Yakubu Datti, ya ce matar ta haifi jaririn ne a hannun ’yan bindigar ranar Lahadi.

Yakubu ya ce bayan sakin matar, ’yan bindigar sun kuma buqaci a ba su ƙarin Naira miliyan ɗaya da rabi kafin su saki ’yar tasu.

“Ka san lokacin da aka sace matar tare da mijinta da ’yar tasu, tana da juna-biyu na kusan wata bakwai. Sai ranar Lahadi da shugaban masu garkuwar ya kira dangin matar ya ce su zo su ɗauki ’yar uwarsu, ta haihu,” inji shi.

Yakubu ya kuma ce ko da dangin suka nemi jin yadda za su yi su ɗauki jaririn, sai ’yan bindigar suka shaida musu cewa ai tuni sun riga sun kashe shi.

“Abinda kawai muka iya yi shi ne mun je mun ɗauko ta a wajen da shaida mana, kuma yanzu haka tana can tana samun kulawa a wani asibiti mai zaman kansa a Kagarko. Yanzu babban ƙalubalen shi ne yadda za a sake tara wata miliyan ɗaya da rabin da za a kai a karvo ’yar matar da ke hannunsu.”

Shi ma Madakin garin na Janjala, Sama’ila Babangida, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar salula, inda ya ce yana cike da takaici a kan batun.

Ya ce yanzu haka yankin nasu ba shi da sakat saboda kusan kodayaushe ’yan bindigar na iya shiga da bindigu su ɗauki mutane yadda suke so.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta magantu ba a kan lamarin.