An taɓa yanke wa wakilin Atiku a Amurka hukuncin ɗauri kan laifin cin zarafi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani wakilin Atiku ɗan ƙasar Amurka mai suna Karl Von Batten, wanda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ɗauka aiki, an taɓa samun sa da laifin cin zarafin budurwarsa tare da yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a watan Disamba na shekarar 2003, kamar yadda takardun kotu da News Point Nigeria ta gani suka bayyana.

Hukuncin ya samo asali ne daga wani lamari da ya faru a watan Yulin 2003, wanda daga baya aka ambata a cikin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ta District of Columbia da ke Amurka.

Cikakken bayani kan hukuncin da aka yanke wa Von Batten ya bayyana ne a cikin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ta District of Columbia, sakamakon wata ƙara da tsohuwar budurwarsa, Cynthia D. Murphy, ta shigar. A cikin takardun kotun, an rubuta sunan Von Batten da “Karl M.E. Okeke.”

Murphy ta shigar da ƙarar ne kan umarnin kariya daga farar hula (Civil Protection Order – CPO) da aka bayar a kanta, bayan ta ƙi barin gidan Okeke duk da cewa ya umarce ta da ta fita.

Umarnin kariya daga farar hula wani umarni ne da kotu ke bayarwa domin hana mutum kusantar wani ko ci gaba da hulɗa da shi.

Murphy ta shaida wa kotun ɗaukaka ƙarar ta Amurka cewa umarnin CPO ɗin bai dace ba, domin shiga gida ba tare da izini ba laifi ne da ya shafi dukiya, ba mutum ba, don haka bai cika sharuddan doka da ake buƙata domin ɗaukar sa a matsayin laifin da ya shafi ’yan uwa ba. Daga bisani, kotun ɗaukaka ƙarar ta soke umarnin CPO da aka bayar kan Murphy tare da umartar ƙaramar kotu da ta janye shi.

A yayin da take yanke hukunci kan ƙarar da Murphy ta shigar, kotun ɗaukaka ƙarar ta Amurka ta bayyana wasu bayanai game da cin zarafin da Von Batten ya aikata.

A cewar kotun, Murphy da Von Batten sun fara soyayya ne a watan Afrilun 2003. Sai dai bayan wasu watanni, dangantakarsu ta fara samun matsala.

A ranar 4 ga Yulin 2003, Okeke ya gayyaci Murphy zuwa wani liyafa a gidansa, inda suka sha abubuwan maye.

A lokacin liyafar, Murphy da Katy Elizabeth Gaire, wadda ke zama a gidan wakilin ɗin, sun shiga banɗaki domin yin wata tattaunawa ta sirri.

Takardun kotun sun bayyana cewa, lokacin da Murphy ta gaya wa Gaire cewa ita da Okeke suna soyayya, Gaire ta ce mata a cikin makonni biyu da ta shigo gidan, ta yi lalata da Okeke har sau huɗu ko biyar.

Bayan Murphy ta ji wannan bayani, sai ta shiga cikin yanayin damuwa, ta fara kuka da ihu.

Lokacin da Murphy ke cikin kuka, Von Batten ya shiga banɗakin, inda su biyun suka fara wata zazzafar gardama.

A yayin gardamar, Von Batten ya umarci Murphy da ta bar gidansa.

Takardun kotun sun bayyana cewa Von Batten ya yi tsalle ya nufi tsohuwar budurwarsa, wadda ke zaune a gefen bahon wanka, lamarin da ya sa ta faɗi.

Daga nan Murphy ta gudu zuwa ɗakin kwanan Von Batten.

Kotun ɗaukaka ƙara ta Amurka ta ce, a cikin ɗakin, Okeke ya ja Murphy ta ƙafafunta da hannayenta, ya rika dukanta a fuska, ciki har da idonta, ya kuma rika shura ta a ƙafafu da duwawunta tare da ture ta jikin bango.

Kotun ta ƙara da cewa, a lokacin da yake cin zarafinta, Okeke ya ci gaba da umartar Murphy da ta bar gidan. Harin ya jawo mata kumburin ido, kumburin fuska, raunuka daga leɓenta zuwa ƙasan wuyanta, da kuma raunuka a gefen fuskarta da hannayenta. Haka kuma, ta samu yanke-yanke a cikin bakinta.

Bayan wakilin ɗin ya fita daga ɗakin, Murphy ta kulle ƙofar sannan ta kira lambar gaggawa ta 911.

A cewar takardun kotun, Murphy ta haura ta tagar ɗakin zuwa wajen ginin bene na farko, saboda tsoron cewa wanda ake zargi zai ci gaba da dukanta.

Lokacin da maƙwabta suka ga Murphy a wajen tagar, sai suka taimaka mata ta sauko.

Daga bisani, tsohuwar budurwar wakilin ɗin ta je Asibitin Jami’ar George Washington domin a duba ta tare da yi mata magani kan raunukan da ta samu.

Sakamakon wannan cin zarafi, an yanke wa Okeke hukuncin ɗaurin kwanaki 180 a gidan yari a ranar 10 ga Disambar 2003.

Kotun ɗaukaka ƙara ta Amurka ta ce, bayan shari’ar laifin ƙarami da aka gudanar a gaban alkali ba tare da alkalai ba, an yanke wa Okeke hukuncin ɗaurin kwanaki 180 kan cin zarafin da ya aikata wa Murphy a ranar 4 ga Yulin 2003.

Sai dai an dakatar da aiwatar da hukuncin ɗaurin, inda aka sanya shi a ƙarƙashin kulawar doka na shekara guda. Haka kuma, an umarce shi da ya nisanci Murphy, ya kammala aikin yi wa al’umma hidima na tsawon sa’o’i 50, ya shiga shirin ba da shawara kan cin zarafin cikin gida, tare da bayar da gudummawa ga Asusun Tallafa wa Waɗanda Laifi Ya Shafa.

Ba a samu damar tabbatar da ko Von Batten ya ɗaukaka ƙarar hukuncin da aka yanke masa ba, domin wasiƙun da aka aika masa domin neman bayani ba su samu amsa ba a lokacin da aka wallafa rahoton.

Dangane da ƙarar da Murphy ta shigar, Kotun ɗaukaka ƙara ta Amurka ta soke hukuncin ƙaramar kotun na bayar da umarnin kariya daga farar hula a kanta, tare da umartar ƙaramar kotun da ta janye wannan umarni.

Alƙalai Anna Blackburne-Rigsby, Stephen Glickman da John Ferren ne suka yanke hukuncin a ranar 3 ga Yulin 2008.

A watan Afrilun 2026, Atiku Abubakar ya ɗauki kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C., wanda ke Washington a Amurka, aiki domin karewa da ƙarfafa abin da ya kira “matsayinsa na mutunci da suna” a Amurka.

Wata takardar rajista ƙarƙashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA), wadda aka shigar wa Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, ta nuna cewa kwangilar aikin lobby ɗin ta kai dala miliyan 1.2 a shekara.

Takardar ta bayyana cewa, daga cikin manufofin ɗaukar kamfanin aikin, akwai karewa da ƙarfafa matsayin Atiku a Washington, tare da daidaita labaran da ake yaɗawa daga masu yi wa Gwamnatin Nijeriya lobby a Amurka.

Tun bayan rattaba hannu kan kwangilar, tarihin rayuwar Von Batten da bayanan da suka shafe shi sun fara fuskantar bincike da tambayoyi daga jama’a.

Sunansa ya haifar da tambayoyi da dama, musamman kan asalin ƙasarsa.

A shafinsa na LinkedIn, an rubuta cikakken sunansa da “Karl-Marɗ Edward Ikemefuna William George Okeke-Von Batten”, wanda ya ƙunshi sunaye masu alaƙa da Birtaniya, Jamus da Ostiriya, da kuma Nijeriya.

Kalmar “Von” sananniyar kari ce da ake samu a wasu sunayen iyalai masu alaƙa da sarauta ko manyan gidaje a Jamus da Ostiriya. Haka kuma, sunan Ikemefuna Okeke na iya nuna alaƙa da yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, yayin da Batten suna ne da ke da asalin Birtaniya.

A cikin takardun kotu kuwa, an bayyana shi da suna “Karl M.E. Okeke”. Haruffan M da E suna wakiltar Marɗ da Edward. Wannan na nuna cewa daga baya wakilin ɗin ya sauya ko ya ƙara wani ɓangare na sunansa zuwa “Von Batten”.

Rahotannin baya-bayan nan sun kuma nuna cewa Von Batten yana amfani da sunaye daban-daban a wasu takardun rajista na Amurka. Misali, an bayyana shi da sunan Karl-Marɗ Okeke-Von Batten a cikin wata takarda ta shekarar 2022, yayin da takardar FARA ta shekarar 2026 da ta shafi Atiku ta bayyana shi da Karl Von Batten.

A kwanakin baya, kamfanin lobby ɗin ya goge wani saƙo da ya wallafa a shafin ɗ, wanda ke sanar da cewa an naɗa Von Batten zuwa wani matsayi a fadar White House.

A cewar kamfanin, Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ne ya naɗa Von Batten a matsayin kwamishina a wata kwamitin shugaban ƙasa da ke ƙarƙashin White House.

A cikin saƙon da daga baya aka goge, kamfanin ya bayyana naɗin a matsayin naɗin shugaban ƙasa, tare da cewa Von Batten ya nuna godiya ga Trump kan amincewar da ya nuna masa. Sai dai kamfanin bai bayyana sunan kwamitin da aka ce an naɗa shi a cikinsa ba.

Har zuwa lokacin wallafa rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga fadar White House da ta tabbatar ko musanta cewa an naɗa Von Batten a wannan matsayi.

By ukarofi

Leave a Reply