Gwamnatin Kano, NASSI da Stanbic IBTC sun shirya taron bunƙasa ƙananan masana’antu

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Zuba Jari, Ciniki, Kasuwanci da Masana’antu ta Jihar Kano ta bayyana cewa taron yini guda da aka shirya domin bunƙasa ƙananan da matsakaitan masana’antu a jihar ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Kano.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taro da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Masu ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta ƙasa (NASSI), wanda Bankin Stanbic IBTC ya ɗauki nauyin gudanarwa a Kano.

Ta ce babban jigon taron shi ne samar da hanyoyin magance matsalolin da ke fuskantar ƙananan da matsakaitan masana’antu, tare da gina yanayi mai kyau na gasa da bunƙasa harkokin kasuwanci a Jihar Kano.

A cewarta, taron ya zo a daidai lokacin da ake matuƙar buƙatarsa, domin manufarsa ta yi daidai da ɗaya daga cikin abubuwan da Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta sanya a gaba, wato samar da yanayin da zai sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

Ta bayyana cewa hakan zai taimaka wa kamfanoni su fara aiki, su dore, su bunƙasa, su ƙirƙiri sabbin abubuwa, su samar da ayyukan yi, tare da yin gogayya cikin nasara da sauran ƙasashen duniya.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar NASSI ta ƙasa, reshen Jihar Kano, Alhaji Aminu Ibrahim Kurawa, ɗan Masanin Ma’ajin Watari, ya yi kira ga ’yan kasuwa da sauran al’umma da su ci gaba da bai wa ƙungiyar goyon baya, domin ta ci gaba da samar musu da damarmakin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana gamsuwarsa da taron, yana mai cewa jami’an hukumomin Gwamnatin Tarayya da na Jihar Kano sun halarta, inda aka gabatar da tambayoyi tare da warware wasu daga cikin matsalolin da ke fuskantar masu ƙananan masana’antu.

Ya ce an kuma gabatar da shawarwari da matakai waɗanda ake sa ran za su taimaka wajen ci gaban masana’antun cikin ɗan lokaci.

Alhaji Aminu Kurawa ya nuna jin daɗinsa kan yadda Bankin Stanbic IBTC ya shiga cikin shirin domin tallafa wa ƙananan masana’antu, yana mai cewa bankin ya yi alkawarin taimaka musu wajen samar da wutar lantarki da kuma samun jari cikin sauƙi.

Ya bayyana cewa matsalar wutar lantarki da ƙarancin jari na daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar masu masana’antu, don haka tallafin bankin zai iya taimakawa wajen rage musu waɗannan matsaloli.

Ya ƙara da cewa sun kuma sanar da Gwamnatin Kano wasu daga cikin matsalolin haraji da suke fuskanta, inda ya ce Gwamnatin ta nuna aniyarta ta ɗaukar matakai domin ganin an magance matsalolin.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Masu ƙananan Masana’antu ta Dakata, Alhaji Zulƙiflu Alhassan Umar, ya bayyana jin daɗinsa da taron da NASSI tare da Bankin Stanbic IBTC suka shirya.

Ya ce taron ya kasance mai matuƙar amfani ga masu ƙananan masana’antu na Dakata, yana mai cewa yankin na daga cikin wuraren da ake samun ɗimbin ƙananan masana’antu a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa taron ya haɗa hukumomi daban-daban, ciki har da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), Hukumar Kula da Ma’auni da Ingancin Kayayyaki (SON) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO).

A cewarsa, an wayar da kan masu masana’antu kan hanyoyin gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, da kuma muhimmancin bin ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa.

Zulƙiflu ya ce masu masana’antu a Dakata suna samun wutar lantarki, amma babban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne tsadar wutar, don haka ya yi kira da a duba hanyoyin sassauta musu farashinta.

Ya kuma bayyana cewa bayan gobarar da ta faru a yankin, masu masana’antun na buƙatar tallafin jari domin farfaɗo da sana’o’insu, yana mai kira ga Bankin Stanbic IBTC da ya taimaka musu wajen samun jari.

A ƙarshe, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa tallafin naira miliyan 10 da ya bai wa mutanen da gobarar ta shafa.

By ukarofi

Leave a Reply