Kwamandan ISWAP ya kashe mataimakinsa saboda harin da sojoji suka kai musu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani Kwamandan ƙungiyar ISWAP, Abu Muhammed, ya kashe mataimakinsa, Abu Darda, bisa laifin yin sakacin da ya kai sojoji suka kai musu hari suka karkashe masa mayaƙa a sansanoninsu.

An kai musu harin ne a sansanoninsu da ke ƙauyukan Mukdolo da Bonei wanda ya kai ga kashe mayaƙa 41, ciki har da Abu-Zahra Munzir.

A rahoton da aka tattaro cewa kwamandan da ya fusata ya kashe Abu Darda a gaban sauran mayaƙan a ƙauyen Kajeri Dogumba da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno.

Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa Abu Muhammed ya zargi Abu Darda da jagorantar hare-haren da ba a yi nasara ba a ranar 19 ga watan Maris a garin Mafa wanda ya yi sanadin kashe ’yan ta’addan da dama tare da kama wasu makamai daga cikin motocinsu.

Kwamandan ya ce suna da manyan motoci uku ne kawai amma Abu Darda ya yi sakacin da har sojojin Nijeriya suka samu nasarar kama su.

Ya ce bai iya waiwaya bayansa ba yayin da har sojoji suka bi sawunsa suka far musu a sansaninsu a lokacin da suke barci suka kai ga kama motocin.

Kwamandan ya ce ya ji zafi musamman saboda sojoji sun kashe mayaƙansa da dama, sun ƙona masa kayan abincinsa da wasu sabbin kayan da aka sayo domin bikin auren da suke shirin yi.

Kwamandan wanda a halin yanzu yake tara mayaƙansa a Kajeri Dogumba, Bula Yagana Aliye a Ƙaramar Hukumar Mafa a Jihar Borno, ya sha alwashin ɗaukar fansa kan kashe mayaƙan nasa da sojojin suka yi.

Dakarun sojojin Nijeriya ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, sun kai farmaki mavoyar ƙungiyar ta’adda ta ISWAP da ke Ƙaramar Hukumar Dikwa a Jihar Borno, inda suka kashe 41 daga cikin ’yan ta’addan ciki har da kwamanda Abu Zahra.