Rahotanni game da kalaman Tedros cewa, Covid-19 na iya ɓulla daga ɗakin gwaje-gwajen Wuhan ba gaskiya ba ne

Daga CMG Hausa

Wasu rahotanni na cewa, a baya-bayan nan babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a asirce cewa, “Mai iyuwa asalin COVID-19 na iya ɓulla daga ɗakin gwaje-gwajen Wuhan.”

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya bayyana Larabar nan cewa, sakatariyar hukumar ta WHO ta yiwa ɓangaren ƙasar Sin ƙarin haske, yana mai jaddada cewa, babban darektan hukumar bai furta irin waɗannan kalamai a bainar jama’a ko a ɓoye ba, kuma bayanan da aka bayar gaba daya ba gaskiya ba ne. Babban darektan da kansa bai amince da abubuwan da suka shafi wannan batu a cikin rahoton ba.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa