Ramadan: Malagi ya bada tallafin buhunan hatsi 1750 ga ’yan gudun hijira a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Mawallafin jaridar Blueprint kuma Kaakaki Nupe, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya kai agaji ga mutanen da ’yan bindiga suka raba da gidajensu a Jihar Neja, tare da bayar da gudunmawar buhunan hatsi 1745 da kuma man gyaɗa wanda kuɗinsu ya kai Naira miliyan 27.

Da ya ke bayar da gudunmawar, Malagi, wanda ya kasance ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, ya ce, an yi hakan ne a cikin watan Ramadan.

Ɗan takarar gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren ƙungiyar Malagi 2023, Barista Bala Marka, ya ce, matakin ya kuma shafi jami’an APC na Jihar Neja.

Ya jajanta wa al’ummar Jihar Neja kan wahalhalun da ’yan bindiga suka shigar da su, inda ya ƙara da cewa, “ina jin baqin ciki kamar yadda kuke ji a cikin wannan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai jiharmu, ina addu’ar mu shawo kan lamarin nan ba da jimawa ba”.

Yayin miqa kayayyakin abincin ga gwamnatin jihar Neja wanda Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Alhaji Ibrahim Inga ya wakilta, Malagi ya kuma jajantawa waɗanda suka rasa ’yan uwansu a harin.

Hakazalika, yayin da ya ke gabatar da kayayyakin har ila yau ga zartarwar jam’iyyar APC tun daga shiyyar zuwa jiha, Malagi ya bayyana cewa, an yi hakan ne domin tallafawa ’yan jam’iyyar.

Da ta ke bayyana kayyakin da aka raba, Marka ta bayyana cewa, ’yan gudun hijirar sun samu buhunan shinkafa da masara da gero guda 450 kowanne da gwangwanin Geri guda 50 da lita 25 na man gyaɗa, yayin da shugaban jam’iyyar APC ya samu jimillar buhu 100 na jihar, buhu 30 na shiyyar, buhu 250 na ƙananan hukumomi da buhuna 1,370 na Unguwa baya ga Naira miliyan ɗaya na sufuri.

Da ya ke bayani, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Haliru Zakari Jikantoro, ya gode wa ɗan takarar gwamna bisa yadda ya ke goyon bayan jam’iyyar da ’ya’yanta a kodayaushe da kuma ’yan gudun hijira, ya ƙara da cewa, a baya Malagi ya bai wa jam’iyyar gudunmawar motoci da kuɗaɗe a cikin jihar.

A nasa jawabin, babban daraktan hukumar ta NSEMA ya yaba da irin wannan karimcin da ɗan takarar ya yi masa inda ya ce wannan shi ne karo na biyu na miƙa tallafin jin ƙai ga ’yan gudun hijira a jihar.

Ya bada tabbacin raba kayan ga mutanen da abin ya shafa na gaske.