Matan da ba su samu mijin aure ba (2)

Daga AISHA ASAS

Barkanmu da sake saduwa a shafin iyali na jaridar al’umma, Manhaja. Idan ba mu manta ba, mun fara shimfiɗa kan darasin mu na yau tun a satin da ya gabata, don haka za mu ɗora daga inda bayanin mu na wancan sati ya tsaya:

Idan kuwa mun amince hakan na faruwa, to ina yake laifi don mace ta rasa mijin aure, ko ta yi jinkiri. A tsangwame ta, a hana ta rawar gaban hantsi, duk don abin da ba ta da iko akan sa. Ba wai ina ƙoƙarin kare duk wata mace da ba ta yi aure ba. Na sani akwai matan da shaiɗan ya riga ya yi masu fitsari a tsakiyar kan su, sun zavi rayuwar sharholiya fiye da shiga daga ciki don mutunta darajarsu. Su waɗannan ba zan ce komai kan su ba, domin dai duniya makaranta ce, rayuwar mace tamkar kayan yayi ce, a lokacin da lokacinsu ke haska wa tamkar ba za a daina yayinsu ba, amma ɗai rana za a wurgar da su a ɗauko wasu, suna ji suna gani ko kyauta wani ba zai saka su ba, wanda idan za ka yi waiwaye, za ka tuna irin daraja da tsada da suke da a idon duniya.

To, haka rayuwarki take a lokacin da kike cikin ganiyar ƙurciyarki ya ke ‘yar’uwa mace, kuma a lokacin kike da zaɓi biyu.

Ɗaya yana hagu, yayin da ɗayan ke dama. Na dama shine, riqe mutuncinki, sanin daraja da ƙimar da Mahalicinki Ya yi ma ki. Rufe kunnenki daga sauraren zugar shaiɗan da ke sanar da ke lokacinki ne, kina da kyau da za ki iya cin duniyarki bisa tsinke komai tsininshi ki wanye lafiya. Tursasa zuciyarki amincewa wannan lokacin ne ya dace ki nemi masoyin gaskiya ta hanyar suturce jikinki, zama ‘yar ƙauye a idon wakilan shaiɗan don samun tabatuwa bisa layin da ba mai iya biyo bayanki sai mutumin kirki.

Zaɓi na biyu, wato hagunki, shine, sa wa ranki son abin duniya da son ganin duniya ta san da ke. Biye wa zamani don ganin ba a kira ki baƙauya ba. Yarda da ke mai kyau ce da ya kamata ki sanar da wanda bai sani ba ta hanyar sakin ni’imar jikinki don mutane su shaida. Mayar da kanki rijiya da kowa zai iya zura guga ya kwashi son ransa don ganin kin tara dukiya ko don biye wa ashararran ƙawaye.

Kowanne ɓangare kika zaɓa kan ki zai sauka, kuma ke za ki girbi abin da kika shuka, domin dai kowa rai ya yi waɗi, aka ce baran mai shi ne. A lokacin da kika zaɓi dama, za ki samu duk wani burin ‘ya mace, amma ba za ki gane ba, sai a daidai lokacin da kika yi bankwana da ƙurciya, kika kai lokacin da duniya ta daina haska ki. A daidai lokacin ne za ki gane babban tanadin da kika yi wa kanki.