Zaɓen mace ko namijin aure (III)

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah da ya sa ke ba ni damar rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja.

Babbar musifar da istimna’i ya ke jawowa ta haɗa da;
1- Rauni da rashin ƙarfin jiki.
2- Raunin ƙwaƙwalwa da kasa riƙe karatu ko kaɗan.
3- Rasa gani da makancewa daga ƙarshe.
4- Karkarwar jiki.
5- Rashin nutsuwa;
6- Yawan tunani.
7- Son warewa waje ɗaya, shi/ita kaɗai.

Malamai sun kawo wasu abubuwa da suke maganin wannan mummunan ciwo mai haifar da miyagun halaye da munanan ɗabi’u kamar haka;

1- Nisantar duk wani abu mai kawo sha’awa, kamar kallon fila-falai da mata suke rawa ko suke sanya kayan da bai dace ba, da duk abin da ya san yana sanya shi jin sha’awa.

2- Shagaltar da kansa da wasu abubuwan, kamar tsara lokutansa, na karatu da na zuwa filin wasa, ya kuma riqa yin wasan motsa jiki, da karanta littattafai kamar na ilimi ko jaridu, da zuwa wajen hutawa da shaƙatawa domin ya samu sauƙin ƙuncin ransa, da ware lokacin da zai riqa yin yawace-yawace a lokacin da ba shi da komai, da yawan karanta Ƙur’ani koda Fatiha ce a kan hanyarsa, da zuwan wajen tarurrukan wa’azi da shirya irinsu, da yawaitar zuwa masallaci a lokacin kowace Salla.

4- Sanya wa kansa ayyukan da zasu cike lokacin hutawarsa.

5- Kula da wasannin motsa jiki kamar gudu a filin wasa, da ɗaga abubuwa masu nauyi da sauransu;

6- Idan akwai lokutan da ya saba aikata wannan mummunan hali a cikinsu sai ya ƙirƙiro wa kansa wani abu daban da zai shagaltar da shi a irin waɗannan lokutan: kamar zuwa hawan sukuwar doki da sauransu.

7- Ya nisanci zama shi kaɗai har abada koda barci zai yi to ya kasance cikin mutane, wato ta yadda idan ba wani abu na lalura ba kamar kama ruwa da bahaya to ba yadda za a yi ya kasance shi kaɗai.

8- Da zarar ya samu yalwa da dama to ya yi maza ya yi aure kada ya jinkirta ko kaɗan.

9- Raya ƙarfin ruhinsa ta hanyar jin cewa zai iya maganin wannan halin da taimakon Allah.

10- Nisantar masu irin wannan hali nasa.

11- Cin abinci mai kyau da tsara lokutan cinsa, ta yadda ba kodayaushe ne zai ci wani abu ba, da kuma wanka da ruwan sanyi a wasu lokuta, da nisantar sanya tufafi masu matse masa jiki.

12- Addu’a da neman taimakon Allah, da jin cewa Allah yana ganin sa duk inda ya ke koda ya shiga ɗaki ya rufe ne shi kaɗai, ya ji cewa kuma Allah zai yafe masa abin da ya yi, kuma ya ɗaukar wa Allah alƙawarin ba zai sake ba.

Za mu cigaba a mako na gaba, Insha Allah.
Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, Ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.