’Yan bindiga sun ba wa mazauna garin Batsari wa’adin mako guda

Daga UMAR GARBA a Katsina

’Yan bindigar da ke ta’addanci a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina sun bai wa mazauna garin wa’adin mako guda, inda su ka buƙaci Sarkin Ruma wato Hakimin Ƙaramar Hukumar Batsari ya shawarci hukumomi don a yi zaman sulhu da su ko kuma su ci gaba da kai wa al’umomin yankin hare-haren ta’addanci.

A Laraba Sarkin Ruma, ya tabbatar da wannan bayanan ga manema labarai, inda ya bayyana cewar kwana huɗu da suka shige, wani Bafillace mai suna Salisu, ya kira shi ta waya, bayan sun gaisa sai ya tambaye shi lafiya? Sai Salisu ya ce, ka turo mutanenka sun kashe mana mutane.

Sai dai Sarkin ya ba shi amsa inda ya ce bai san an kashe kowa ba, amma zai bincika.

Rahotannin da Manhaja ta samu sun nuna cewar ‘yan bindigar su na magana ne akan wani lamari da ya faru, inda ‘yan bindigar suke zargin ‘yan sanda da kashe ma su mutane biyu a Katsina, lamarin ya faru ne bayan da wani ɗan sanda ya shiga motar haya tare da wasu ‘yan ta’adda sai ya ji suna waya suna cewa ga su nan cikin wata mota mai kama kaza da kaza an yi zargin su na waya da sauran abokan ta’addancinsu ne, nan da nan ɗan sandan ya fahimci abin da ke gudana, sai ya haɗa su da ‘yan banga don a bincike su daga bisani mutanen su ka mutu hannun jami’an tsaro, inda daga bisanii aka gane ma su garkuwa da mutane ne kamar yadda majiyar Manhaja ta samu labari.

Sarkin ya kuma bayyana cewar Salisun ya ce ya ba shi kwana bakwai ya sa a yi sasanci, in ba haka ba za su far musu.

A baya dai ‘yan bindiga sun taɓa barazanar za su kawo wa garin hari bayan sun kira ta waya sun sanar sai ga shi kuma sun cika alƙawari, inda su ka kutsa kai a Unguwar Katoge su ka yi ta’addanci wanda yai sanadiyyar rasa ran wani mutum ɗaya tare da sace wasu fiye da ashirin kafin su sako su bayan shafe watanni a hannun su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya  tabbatar wa majiyar Manhaja da faruwar hakan, inda ya bayyana cewar ta kafar sadarwar zamani su ma suka ji cewa ana yaɗa  jita-jitar ‘yan bindiga sun aika da takarda cewa za su zo su ɗauki fansa.

Sun kuma ji labarin cewa mutanen Batsari sun kame wasu da ake zaton ‘yan ta’adan ne, kuma DPO a Katsina ya je ya kwashe su, amma daga baya mutum biyu sun mutu a asibiti. Wannan fargabar ne ya jawo jita-jitar.

Ya ƙara da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarni da abinciki gaskiyar lamarin.

Ɓarayin daji da aka fi sani da ‘yan bindiga sun addabi wasu daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Katsina, inda a wasu lokuttan su kan ɗora wa al’umomin da ke kusa da maɓoyarsu haraji tare da yi masu barazanar za su kawo masu hari idan ba su haɗa wani adadin kuɗin da su ke buƙata ba, sai dai wannan karon sun fito da sabon salo na neman a yi zaman sulhu da su wanda al’ummar jihar ke ganin wani sabon salon yaudara ne.

Daga ƙarshe SP Isa ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, domin an umarci ‘yan sanda da su sa ido don gudun abin da ka je ya dawo.