Za mu yi ƙoƙari wajen samar da ƙwararrun likitocin haƙora – Masarautar Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ta bayyana cewa za ta wayar wa ɗalibai da kan wajen ganin sun koyi ilimin kula da lafiyar hakora.

Masarautar ta ƙudirin aniyar yin wannan aiki la’akari da muhimmancinilimin da kuma ƙarancin likitocin haƙora a Kano dama Arewacin Nijeriya baki ɗaya.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai Martaba Sarki kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda  Ɗan Goriban Kano, Alhaji Abubakar Sule Gaya ya wakilta a wajen taron Ƙungiyar Ɗalibai masu Neman Zama Ƙwararrun Likitocin Haƙora na Nijeriya (NADS) suka gabatar da taron su a Jami’ar Bayero da ke Kano ranar Litinin da ta gabata.

Shi ma Alhaji Muhammad Giɗaɗo Muhammad, Mataimakin na musamman kan harkar karɓar baƙi na masauaratar Kano kuma Sakataran kula da ƙungiyar NADS da masarautar ta naɗa don tattaunawa da masarautar Kano da ɗaliba  da suka nemi taimako da haɗin kan masarautar Kano, ya ce masarautar ƙarƙashin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero za ta yi iya ƙoƙarinta ta taimaka da shawarwari da abin da ya kamata domin jama’a su fahimci muhimmancin ilimin da kuma lura da lafiyar bakin su da haƙoran su.

Haka kuma ya yaba wa ƙungiyar kan tallafa wa jama’a da ta yi kan duba lafiyar haƙoran su kyauta a wannan lokaci.

Ɗaliban dai sun zo ne daga wurare daban-daban na ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin shugabanta da mataimakin sa Wisdom Okereke, sai shugaba mai kula da Arewa na ƙungiyar Umar Aliyu Umar da taimakon Dakta Khalid.

Sai dai wani mai lura da al’ammuran yau da kullum ya shawarci ƙungiyar NADS kan girmama al’adu da addini, wanda shi ne babbar manufar masaurautar Kano da al’ummarta.