‘Yan sandan Amurka sun lalata haƙƙoƙin jama’a

Daga AMINA XU

Abokai sannunku! yau na zana wani Cartoon dangane da yadda ‘yan sandan Amurka da ke keta haƙƙin bil Adam, abin da na zana ya auku ne a shekarun baya-bayan nan a birnin Kansas na jihar Missouri ta Amurka. Amma ‘yan sandan ba su daina ɗaukar irin waɗannan matakai ba, a kwanan baya sun sake aikata hakan kan wata yarinya mai shekaru 12 a duniya, ƙasa da shekaru 2 da rasuwar George Floyd, wanda ya mutu a sakamakon uƙubar da ‘yan sanda suka yi masa. Ko ba su damu da haƙƙin Bil Adam ba ne?

Matakin da ‘yan sanda suka dauka ya lalata haƙƙoƙinsu. Ban da haka, sunan ‘yan sanda Amurka ya baci sosai saboda yiwa fursunoni azaba a gidan kurkuku, idan ba a manta da abin dake faruwa a gidan kurkuku na Guantanamo ba. Laifi tudu ne, Amurka ta taka nata tana hangen na saura. Ya kamata ta yi ƙoƙarin daidaita matsalolinta kafin ta tsoma baki kan harkokin haƙƙin Bil Adama na sauran ƙasashe.

Mai zane: Amina Xu