Ramadan: Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta ba da tabbacin inganta tsaro a jihar

Daga RABI’U SANUSI a Kano.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta shelanta wa al’ummar jihar musamman musulmai, ci gaba da samar da ingantaccen tsaro a faɗin jihar a lokacin azumi da ma bayansa.

Wannan tabbaci na ƙunshe ne a wata sanarwar manema labarai da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, kasancewar Jihar Kano kan gaba a fagen kasuwanci, jihar na fuskantar ƙarin baƙi daga ciki da a wannan lokaci.

Ya ce don haka hukumar ta gyara ɗamararta don inganta sha’anin tsaro a faɗin jihar, tare da kira ga jama’a da su zama masu bin doka da oda.

Sanarwar ta ƙara da cewa, batun dokar masu a-daidai-ta-sahu da hukumar ta sanar kwanan baya tana nan daram.

Ta ce sauran jami’an tsaro a jihar za su ci gaba da sanya ido da kuma kama waɗanda suka karya dokar.

“Dokokin sun hadar da dokar masu a-daidai-ta daga ƙarge 10 na dare zuwa shida, sai dokar hana hawan dawakai da sunan kilisa, kazalika dokar hana buga ‘nokout’ ko ‘bangas’ ita ma tana nan, za a kama tare da hukunta wanda ya take ta.”

A cewar sanarwar, masu zuwa masallatai dan gudanar da ibada kamar wa’azi a lokacin wannan wata dole sai an sa kula da masu zuwa da dawowa su zama masu sanar da jami’an tsaro, kuma sun bayyana bin umarni da masu tuƙin ababen hawa tare da kauce wa tuƙin ganganci da kauce wa gudu a kan tituna da ke haifar da haɗari.

Kwamishinan ya roƙi al’ummar Kano da su ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya tare da sanar da jami’an tsaro dukkan wani motsi da ba su yarda da shi ba ko kuma su sanar da jami’an tsaro ta wannan lambobin 08123821515,09029292926,08032419754.

Daga ƙarshe, CP Mamman Dauda da sauran jami’an tsaro suna yi wa al’ummar jihar barka da shigowar watan azumi tare da fatan samun babban rabo.