Zargin garkuwa: ’Yan sanda sun ceto yara bakwai, sun kama wasu mutum uku a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da yara a Ƙaramar Hukumar Suleja ta jihar.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya fitar, wanda kuma aka rabawa manema labarai a Minna a daren Juma’a, ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a Abuja.

“Waɗanda ake zargin, Savior Ebuka ɗan shekaru 20 da Mary Peter 25, a Tunga-Maje ta unguwar Gwagwalada da ke Abuja, da dai sauransu.

Ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin suna da hannu wajen garkuwa da wasu ’yan uwa biyu masu shekaru 3 da 5 a gidansu da ke Suleja a Jihar Neja a bara.

“Idan za a iya tunawa, a ranar 20/10/2022 da misalin ƙarfe 11:25 na safe, an samu rahoton wani lamari na sace wasu yara biyu a ‘B’ Div. Suleja. A ranar 19/10/2022 da misalin ƙarfe 2100, wasu yara biyu ’yan shekara 5 da 3 na miji da mace na unguwar hukumar ruwa ta Suleja sun ɓace wanda wani sabon ɗan haya ne ya tafi da su.

Wasiu ya bayyana cewa, bayan waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da yaran ne suka kai su wani gida da ke Abuja inda suka buƙaci wasu kuɗaɗe.

Abiodun ya bayyana cewa, an mayar da yaran zuwa wani gidan marayu da ke Lugbe, Abuja inda daga ƙarshe ’yan sanda suka ceto su.

“Jami’an ’yan sandan sun ƙara ƙaimi wajen binciken inda daga bisani suka gano wani mai suna Chinwe Egwu mai shekaru 49 a unguwar Lugbe Abuja a matsayin mai kula da yaran ba bisa ƙa’ida ba.

Kakakin ’gan sandan ya ƙara da cewa, an miƙa sauran yaran biyar da aka ceto tare da ’yan uwan biyu ga sashin jin daɗin jama’a na Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya ƙara da cewa, ana ƙolarin cafke sauran waɗanda ake zargin gabaɗaya.

“Ana ci gaba da ƙoƙarin kama Ifeoma da Patience domin cigaba da gudanar da bincike, kuma waɗanda ake zargin zuwa yanzu za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an gudanar da bincike.