Ranar Agajin ɗan Adama: Caritas ta buƙaci ƙasashen duniya su kai ƙarshen tashin hankali

Spread the love

A yayin bikin Ranar Agajin Bil-Adama a ranar 19 Agusta, ƙungiyar Caritas Internationalis, wacce ita ce reshen agaji na cocin Katolika, ta yi kira ga shugabannin duniya da su kawo ƙarshen tashin hankali da rikice-rikice da ke addabar al’umma.

Caritas ta tuna da mutuwar ma’aikatan agaji 22 a harin bam da aka kai ofishin Majalisar ɗinkin Duniya a Baghdad a 2003, wanda ya zama dalilin kafa wannan rana ta tunawa. A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa, sama da ma’aikata 380 aka kashe a fagen agaji a shekara ta 2024 a ƙasashe daban-daban, kuma lamarin na ƙara ta’azzara a 2025.

Ta kuma yi kira ga gwamnatoci da su kare ma’aikatan agaji da fararen hula, tare da girmama mutuncin kowane ɗan-adam. Caritas ta jaddada cewa, wannan rana ba wai ta tunawa da mamata kaɗai ba ce, har ma da kira ga aiki da ɗaukar matakai domin tabbatar da cewa ba a sake zubar da jininsu a banza ba.

By ukarofi