Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmummin Jibrin, ya roƙi mutanen Arewa su mara wa ƙudurin dokar sake fasalin haraji baya da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya kawo.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana a ranar Lahadi a cikin shirin talabijin na Channels.
Dan majalisar wanda ɗan jami’iyyar NNPP ne, ya ce ƙudurin na ƙunshe da abubuwa da dama da yankin Arewa za ta amfani da su.
“ƙudurin ya ƙunshi wasu matakan ba wa jihohin Arewa kariya kowanne irin abun da ka iya cutar da su.
“Waɗannan matakai na da muhimmancin gaske wajen kare muradan yankin Arewa saboda ko da an sake fasalin harajin, Arewa ba za ta fuskanci wani ƙaluble ba,” inji Jibrin Kofa.
Watanni biyu da suka wuce, shugaba Tinubu ya aike wa da majalisun ƙasar nan wani ƙuduri doka da yake neman sahalewarsu.
Sai dai waɗannan ƙudurin dokokin sun gamu da cikas inda ƙungiyar gwamnonin Arewa a yayin wani taro da suka yi a Kaduna a watan da ya gabata, sun soki lamarin ƙundurorin musamman na harajin ɓAT wanda suka ce ya ci karo da wasu muradan Arewa. Wannan ta sa gwamnonin ba wa ‘yan majalisun jihohinsu umarnin yin watsi da wannan ƙuduri.
ɗaya daga cikin ƙudurin dai ya ƙunshi sauya fasalin harajin ɓAT ta hanyar rage abin da gwamnatin tarayya ke samu daga kaso 15% zuwa 10%.
Sai dai ƙudurin ya ƙunshi bayanin tsarin yadda za a kasafta harajin da ake samu a kowacce jiha.
Haka kuma majalisar zartarwa ta tatalin arziƙi, wacce ta ƙunshi gwamnonin da mataimakin shugaban ƙasa, ta buƙaci shugaban ƙasa ya janye wannan ƙuduri daga gaban majalisun kasar nan.
Sai dai shugaban ƙasa ya yi kunnen uwar shegu da buƙatar tasu inda ya ce a bar majalisa ta yanke hukunci.
A majalisar kuwa, sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Barno ta Kudu, shi ne jagaba wajen ƙalubalantar ƙudurin.
A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Ndume, ya ce wannan ƙuduri ya makara domin ba wanda aka tuntuɓa a kai.
Har zuwa yanzu dai wannan kuduri yana kan matakin karatu na farko a majalisun ƙasar nan.
Haka ma ko da a watan da ya wuce, kwamitin kuɗi na majalisun sun zauna da shugaban hukumar tattara haraji na ƙasa domin duba lamarin.
A yayin da yake magana kan ƙudurin, mista Jibrin, wanda tsohon shugaban kwamitin duba kashe kuɗaɗen gwamnati, ya ce, babban ƙalubalen da kudurin ke fuskanta shi ne kasancewar shugaba Tinubu ya gabatar da shi domin shi an san shi masanin haraji ne.
Kuma da yawa daga cikin masu ƙalubalantar ƙudurin har yanzu ba su kai ga karanta su ba.
“Mutane suna ji an ce sake fasalin haraji, sai suka tsorata ba tare da sanin abin da ƙudurin ya ƙunsa ba da yadda zai shafe su.” In ji Kofa.
Daga nan ya roƙi sauran ‘yan majalisun ƙasar nan da su fara duba cikakken rubutaccen ƙudurin kafin su yanke hukunci.
“Idan ka kalli ƙudurin ba wai yana magana ba ne kan lafta wa talakawa sabbin haraji ba ne, ƙudurin ya ƙunshi yin gyara ne ga tsarin yadda al’amuran harajin suke a Nijeriya,” inji Jibrin Kofa.
