Rashin haɗuwar tawagar alƙalan New York ya tilasta ɗage tuhumar Trump

Batun tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban Amurka Donald Trump a game da bai wa wata jarumar fina-finan batsa maƙudan kuɗaɗe a matsayin toshiyar baki don kada ta tona abin da ta ce ya taɓa shiga tsakaninsu ya ɗauki sabon salo a ranar Laraba, bayan da tawagar alƙalan birnin New York ta gaza zama kamar yadda aka yi tsammani, lamarin da ya tilasta ɗage yanke hukuncin zuwa mako mai zuwa.

Tun bayan da tsohon shugaban na Amurka Donald Trump da kansa ya sanar da cewa ana shirin kama shi a wannan makon, lamarin da ya sanya raɗe-raɗin yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

A Larabar nan, wani babban jami’in tsaro da ba a bayyana sunansa ba ya shaidawa akasarin kafofin yaɗa labaran Amurka cewa, an ɗaga zaman tsaida shawarar a gurfanar da tsohon shugaban ko akasin haka, lamarin da jaridar ‘The New York Times’ ta bayyana a matsayin basa-bam-ba.

Tawagar alqalan wadda ta saba zama a ranakun Alhamis wata majiya da ke kusa da lamarin, wanda ya kawo labarin daga zaman ya ce, zai yi wuya a yi wani zama a wannan makon, abin da ya sa ake tunanin zai iya kai wa makon gobe.

Trump mai shekaru 76 zai kasance shugaban Amurka na farko, tsoho ko mai ci, wanda aka tava tuhuma da aikata laifi a gaban kuliya, idan har tawagar ta kaɗa ƙuri’ar goyon bayan tuhumarsa.

Ana tuhumar Trump da aikata laifuka da dama da suka haɗa da yin jayayya da kayen da ya sha a zaɓen shugaban ƙasa na 2020, da kuma ingiza magoya bayansa su yi kutse a ginin majalisun dokokin ƙasar.

Wasu na ganin wannan matsalar da ya shiga ka iya zama ƙarfen ƙafa ga ƙoƙarinsa na sake takarar shugaban ƙasa a shekarar 2024.